An Cafke Wani Matashi Kan Zargin Satar Kodar Wani Yaro Tare Da Siyarwa A Abuja
- Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani matashi da ake zargi da sace kodar wani yaro ba tare da saninshi ba
- Wanda ake zargin ya yaudari yaron ne tun daga jihar Benue har Abuja tare da saka wa a masa tiyata da siyar da kodar
- Alkalin kotun, Taribo Atta ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a babban gidan kaso da ke jihar Benue
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Jami’an tsaro sun cafke wani da ake zargi da satar kodar wani matashi a birnin Tarayya, Abuja.
Wanda ake zargin mai suna Aondoaseer Agbadu, wanda bai wuce shekaru ashirin ba ya yaudari dan shekara 17, Terungwa Swati tare da sace masa koda.
Ta yaya matashin ya yaudari mai kodar?
Ya yaudari yaron tun daga jihar Benue har zuwa Abuja inda ya hada baki da wasu aka yi masa tiyata tare da cire kodar aka kuma siyar bai sani ba, cewar Daily Trust.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jami’in dan sanda da ya gabatar da kara, Sifeta Godwin Ato ya fadawa kotu cewar ana farautar sauran wadanda ake zargi da aikata wannan mummunan aiki.
Godwin ya ce mahaifin wanda aka cire wa kodar ya kawo kara ofishin inda ya bayyana yadda su ka yaudari dan nasa tare da cire masa koda.
Mahaifin wanda ke zaune a karamar hukumar Gwer ta jihar Benue ya ce hakan cin zarafi ne kuma an siyar da kodar ba tare da saninshi ba.
Wane hukunci barawon kodar ya fuskanta?
Yayin da dan sandan ya bayyana cewa wannan laifi na matasan ya sabawa dokar kasa ta haramta safarar dan Adam.
Ya ce a yanzu haka rundunar ‘yan sanda a jihar na ci gaba da bincike kan lamarin don gurfanar da su a gaban kotu, People's Gazette ta tattaro.
Alkalin kotun, Taribo Atta bayan sauraren korafe-korafen ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan kaso da ke Makurdi da ke jihar Benue.
Har ila yau alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 23 ga watan Oktoba na wannan shekara da mu ke ciki.
An damke ma’aikaciyar asibiti mai sayar da mahaifa
A wani labarin, an cafke wata ma'ikaciyar asibiti mai suna, Fatima Sulaiman kan zargin siyar wa wani malami mahaifa domin amfani da shi.
Ta kara da cewa matar malamin kawarta ce kuma kimanin watanni biyu da suka gabata malamin ya bukaci ta kawo masa.
Asali: Legit.ng