Matar Tinubu Ta Raba N500m da Rikici Ya Barke, Babu Musulmi 1 da Ya Amfana

Matar Tinubu Ta Raba N500m da Rikici Ya Barke, Babu Musulmi 1 da Ya Amfana

Jama’atu Nasril Islam ta soki yadda aka zabo wadanda za su ci moriyar gudumuwar Remi Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Uwargidar shugaban Najeriyan ta bada taimakon N500m a Filato, amma ba a tuna da musulmai ba

Kungiyar ta ce an yi sonkai duk da an hallaka musulmai da yawa da ake fama da kashe-kashen

Abuja - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI ta reshen jihar Filato, ba ta ji dadin yadda za ayi rabon gudumuwar kudin da Remi Tinubu ta bada ba.

Kungiyar addinin musuluncin tayi bayanin yadda aka maida mutanenta saniyar ware a zaben wadanda za a ba kudin, Daily Trust ta kawo rahoton.

A farkon makon nan uwargidar shugaban Najeriya ta ziyarci Filato domin jajantawa mutanen da aka kashe a sanadiyyar rikici a wasu garuruwa.

Remi Tinubu
Uwargidar shugaban Najeriya, Remi Tinubu Hoto: @oluremitinubu
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Mai Dakin Tinubu Ta Yi Kyautar Ban Mamaki, Ta Rabawa Mutane N500m a Filato

Babu dangin musulmai a Filato?

Nan take Sanata Remi Tinubu ta ware N500m domin mazauna kananan hukumomin Mangu, Bokkos, Barikin Ladi, Riyom da kuma Jos ta Kudu.

JNI ta bakin Darektanta na harkokin ICT/NGO, Lawal Ishaq, ta yi zargin cewa babu alamar kamanta adalci a wajen yin rabon wannan gudumuwa.

Ishaq wanda ya ke lura da sha’anin fasahar zamani da kungiyoyi masu zaman kansu, ya ce ko musulmi daya babu a sunayen wadanda za a ba kudin.

Laifin Gwamnatin Filato ne ba Remi Tinubu ba

Kungiyar addinin ta na zargin gwamnatin jihar Filato da kin yin abin da ya kamata domin ganin an kawo karshen rigingimun da ke yawon barkewa.

Daily Nigerian ta ce JNI ta na zargin gwamnatin jiha na da hannu wajen zakulo wadanda za a rabawa miliyoyin da uwargidar shugaban kasa ta bada.

Jawabin kungiyar JNI

“Jagororin musulunci da-dama da kuma Fulani makiyaya sun nuna rashin jin dadinsu da takaici game da yadda karara aka kebe musulmai, aka yi son kai a jerin dangogi 500 da rikicin da aka yi kananan hukumomin jihohin Filato ya shafe su.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

A wajen shugabannin musulmai da Fulani da-dama, a lokacin da gwamnatin jihar Filato ta fito da jerin sunayen wadanda za su amfana, babu musulmi ko guda.
Wannan abin takaici ne domin musulmai da yawa, har da makiyaya Fulani su na cikin wadanda rikicin ya shafa musamman a Mangu, inda rigimar ta dauki salon addini.”

- Malam Lawal Ishaq

N1 za ta koma $1 a Najeriya?

Ana jita-jitar za a karfafa Naira a Najeriya, sai ga farashin Dala ya doshi N1000 a kasuwar canji kuma CBN ta karyata rade-radin da ke yawo.

Akwai kafa ta musamman da bankin CBN ya samar domin masu bukatar kudin ketare domin su shigo da kaya, a nan Dala ta haura N770.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng