Bindigar Tashar Kainji/Jebba Ta Jefa Miliyoyin Mutane a Duhu Inji Ministan Wuta

Bindigar Tashar Kainji/Jebba Ta Jefa Miliyoyin Mutane a Duhu Inji Ministan Wuta

  • Adebayo Adelabu ya fito ya yi dogon bayani a game da durkushewar babban layin wutar lantarki
  • Ministan ya ce tangardar ta fito ne daga tashar Kainji/Jebba 330kV bayan an ji karar tarwatsewa
  • A lokacin, ma’aikata su na ta kokarin ganin al’umma sun fita daga kangin duhun da su ka shiga

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce matsala aka samu a tashar Kainji/Jebba 330kV, hakan ya yi sanadiyyar da aka fuskanci rashin lantarki.

Ministan harkokin wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi karin haske a jeringiyan bayanai da ya fitar a dandalin Twitter a ranar Alhamis.

Bayanan Adebayo Adelabu sun zo kenan sai aka samu labari an kama hanyar gyara wutan, a ra'ayinsa nan da shekara guda za a gyara wuta.

Ministan Wuta
Ministan lantarki, Adebayo Adelabu a taron FEC Hoto: @BayoAdelabu
Asali: Twitter

Tashar Kainji ta jawo lantarki ya koma 0MW

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya

Ministan ya bayyana yadda tashar Kainji ta jawo wutan lantarkin kasar ya durkushe, aka rasa komai, wannan ya jawo ko ina ya zama din-dim.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Da karfe 00:35 na safiyar yau, aka samu matsalar wuta a dalilin karar fashewar wani abu da aka ji a tashar Kainji/Jebba 330kV (Cct K2J), an ga tsanwar layin lantarki Kainji/Jebba 330kV ta kone.
Hakan ya jawo saukar nauyi daga 50.29Hz zuwa 49.6Hz 7 da karfe 0:35:06 na safe inda aka yi asarar megawatt 356.63 a Jebba.
Da karfe 00:41 na safen, karfin ya sake sauka daga 49.37 Hz zuwa 48.41 Hz hakan ya jawo na’urar ta durkushe."

- Adebayo Adelabu

Ma'aikata na kokarin dawo da wuta

A lokacin da ministan tarayyan yake bayani, ya tabbatar da cewa ana bakin kokarin ganin komai ya yi daidai ta yadda jama’a za su dawo cikin haske.

Kara karanta wannan

Ahaf: Rashin Gaskiya Ta Sa Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP a Kano, An Ba Dan Takarar APC

"Ina mika godiya ga uk wadanda su ka nuna damuwarsu ko su tanka ta hanyoyi dabam-dabam da kuma injiniyoyi saboda gaggawar daukar matakinsu da kuma aikin da su ka yi zuwa yanzu.
Sai mu yi gaggawar kammala dawo da wutan ba tare da bata lokaci ba."

-Adebayo Adelabu

Jawabin ministan ya ce da gan-gan gwamnatin tarayya ta yi tsit ba tare da cewa komai ba, dalili kuwa saboda gudun miyagu su yi amfani da damar.

Ina labarin matatar Dangote?

Tun tuni aka ce Najeriya za ta daina dogara da wasu kasashe wajen samun fetur, ana da labari har yau kamfanin NNPC ne yake shigo da mai daga ketare.

Matatar Dangote da aka kaddamar ba ta fara aiki ba tukuna. Kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis aka bude ta da niyyar fara tace mai zuwa Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng