An Bar Najeriya Babu Kowa, Tinubu da Kashim Shettima Duk Sun Tafi Kasar Waje

An Bar Najeriya Babu Kowa, Tinubu da Kashim Shettima Duk Sun Tafi Kasar Waje

  • Yanzu haka Kashim Shettima ya tafi kasar Cuba, zai wakilci Bola Ahmed Tinubu a taron ‘Yan G77
  • Shugaban kasa da Mataimakin shugaban kasar sun tafi ketare domin kawowa Najeriya cigaba
  • Daga taron G20 a Indiya, Bola Tinubu ya wuce kasar UAE a lokacin da Shettima ya tafi birnin Havana

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Najeriya domin wakiltar Bola Ahmed Tinubu a taron G77 a Havana a Cuba.

Darektan yada labarai na ofishin Mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, ya fitar da jawabin da ya sanar da haka a farkon makon nan a Abuja.

Mista Abiola ya ce za ayi taron ne daga ranar Juma’a zuwa Lahadi, The Cable ta kawo rahoton.

Kashim Shettima
Kashim Shettima wajen taron BRICS Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Meya kai Najeriya taron G77

Bayanin ya nuna taron na G77 zai taimaka a shawo kan matsalolin da su ka shafi kasashen da ke cikinta, Najeriya na cikin wadanda suka kafa ta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ministan Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa Kan Muhimmin Batu, Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Najeriya na cikin iyayen kungiyar G77 da kasashe 67 masu tasowa su ka kafa a shekarar 1964.”
“Kungiyar – Wata gamayyar kasashe 134 masu tasowa masu dauke da 80% na al’ummar duniya na burin tallata manufofin cigaban tattalin arziki kuma a samar da karfin sasantawa da majalisar dinkin duniya.”

- Olusola Abiola

'Yan rakiyar Shettima

Rahoton ya ce ministan gona da raya karkara, Abubakar Kyari, ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji su na cikin ‘yan tawagar Kashim Shettima.

Wani babban jami’i da aka dauka shi ne sakataren din-din-din na ma’aikatar waje, Adamu Lamuwa. Zuwa karshen makon nan ne za su dawo gida.

Shugaban kasar Cuba, Miguel Díaz-Canel, zai jagoranci taron a matsayinsa na shugaban G77.

Shettima zai kebe da shugabannin duniya domin jawo hannun jari a madadin Bola Tinubu wanda shi kuma ya tafi dunkulalliyar daular Larabawa.

Kara karanta wannan

An Cire Takunkumi: Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Daga Zama Da Shugaban UAE

Shugaban majalisar dinkin duniya zai halarci zaman shekarar nan wanda takensa ya kunshi rawar kimiyya, fasaha da kirkira wajen kawo cigaba.

Tasirin zuwan Tinubu UAE

Kun ji labari Bola AhmedTinubu ya shawo kan UAE, an janyewa 'Yan Najeriya haramcin shiga Kasar Larabawan a sakamakon sa bakin da aka yi.

A lokacin gwamnatin baya, alaka tayi tsami tsakanin kasashen biyu. Za a cigaba da zuwa birnin Dubai bayan jirage sun daina tashi a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng