Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addini Da Wasu Mutum 3 a Jihar Filato
- Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki yankin Maigemu a karamar hukumar Jos ta gabas a jihar Filato
- Maharan sun yi awon gaba da malamin addini da wasu mutane uku bayan sun bude wuta a iska
- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwa al'amarin inda ta ce jami'anta suna bisa kan aiki kan lamarin
Jihar Plateau - Al'ummar yankin Maigemu da ke karamar hukumar Jos ta gabas a jihar Filato sun shiga rudani a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, lokacin da yan bindiga da yawansu suka farmake su tare da sace wani malamin addini da wasu mutum uku.
Yadda yan bindiga suka sace malamin addini da wasu uku a Filato
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindigar sun farmaki cocin ECWA da ke Nuku a yankin da misalin karfe 5:40 na asuba sannan suka yi awon gaba da malamin addini a gidansa. An yi awon gaba da shi a kan idon iyalinsa.
Wani jigo a garin ya bayyana cewa yan bindigar wadanda suka ci karensu ba babbaka na kusan mintuna 40, sun kuma yi awon gaba da wasu mutane uku, Usman Umaru, Agwom Dauda, da wata mata mai suna Sarah.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyar ta kuma bayyana cewa yan bindigar wadanda suka yi harbe-harbe a iska don hana mutane, musamman yan banga da maharba fitowa don ceton mutanen sun tafi da wadanda suka sacen a cikin wata mota yayin da saura suka bi baya a baburansu.
An tattaro cewa jami'an tsaro, yan banga da maharba suna kakkabe tsaunuka a cikin yankin da nufin kama masu garkuwa da mutanen da abokan huldarsu da ke addabar karamar hukumar.
Wani dan uwan malamin wanda ya zanta da jaridar The Nation bisa sharadin sakaya sunansa ya bayyana cewa maharan basu tuntubi yan uwansu don neman kudin fansa ba.
Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito
Rundunar yan sanda ta yi martani kan sace malamin addini
Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da lamarin.
Alabo ya ce jami'an rundunar na kan lamarin domin kama wadanda suka aikata ta'asar, rahoton Nigerian Tribune.
Yan bindiga sun kashe fastoci 23 tare da rufe cocina sama da 200 a Kaduna, CAN
A wani labarin, mun ji cewa kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta ce yan bindiga sun kasge akalla fastoci 23 kuma an rufe cocina guda 200.
Kamar yadda SaharaReporters ta rahoto, shugaban kungiyar CAN a Kaduna, Rev. John Hayab, ne ya bayyana haka a wani taron gaggawa tare da kwamishinan yan sanda na jihar, Musa Garba da fastocin jihar a ranar Talata, 12 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng