Sakacinka Ya Yi Yawa: Gwamnan Kano ya Bada Dalilin Dakatar da Jami’i Daga Kujerarsa

Sakacinka Ya Yi Yawa: Gwamnan Kano ya Bada Dalilin Dakatar da Jami’i Daga Kujerarsa

  • Gudumar Gwamnan jihar Kano ta fada kan shugaban hukumar KASCO, yanzu an dakatar da shi
  • Abba Kabir Yusuf ya na tuhumar Tukur Dayyabu Minjibir da saida kayan da gwamnati ta mallaka
  • Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce takardar dakatar da jami’in ta fito ta ofishin Abdullahi Baffa Bichi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya sanar da cewa ya dakatar da shugaban hukumar KASCO, Tukur Dayyabu Minjibir.

Sakataren yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa cewa an samu jami’in da sakaci a wajen aiki.

Sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa ta ce Mai girma Abba Kabir Yusuf ya dauki wannan mataki saboda kawo karshen rashin gaskiya.

Abba Kano
Abba Gida Gida Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa
Asali: Facebook

Jawabin Sanusi Bature Dawakin Tofa

"A cikin yunkurinsa na yakar rashin gaskiya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin ayi gaggawar dakatar da shugaban KASCO, Tukur Dayyabu Minjibir

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Neman Dawowa Ɗanye, Tsagin Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi Ga Wike

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya bada umarnin aika takardar dakatarwar ne a wata wasika ta ranar 12 ga Satumba 2023 wanda sakataren gwamnati, Dr. Abdullahi Bichi ya aika."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Premium Times ta ce ana zargin Tukur Minjibir da saida da hatsin da gwamnatin Kano ta mallaka.

Tsige Tukur Minjibir a KASCO

A sanadiyyar haka, Minjibir zai mika ragamar hukumar samar da kayan gonan zuwa ga babban jam’in da ya fi matsayi omin a gudanar da bincike.

Kamar yadda Abdullahi Bichi ya bayyana a wasikar, makomar Dr. Minjibir ta na ga binciken da za a gudanar domin gano gakiyar zargin da ake yi.

Da Salisu Yahaya Hotoro ya bada sanarwar a Facebook, mutane da-dama sun tofa albarkacin bakinsu, su ka ce gwamnan ba da wasa yake yi ba.

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

Dr. Tukur Minjibir ya na cikin wadanda gwamnatin Abba Yusuf ta ba mukami a watan Yuli, a yanzu bai kai watanni biyu da fara aiki a KASCO ba.

Tallafin da aka raba a Jihar Kano

Ana da labari Gwamnatin Kano a karkashin Abba Gida Gida za ta raba buhunan shinkafa fiye da 270,000 da kananan buhunan masara 160, 000.

Nakasassu, marasa karfi da ma’aikatan da ke kananan hukumomin jihar Kano sun ci moriyar rabon, haka zalika manoma da matan kauye za su amfana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng