Fitacciyar Jami'ar Najeriya Ta Kara Kudin Makaranta Ana Cikin Wahala
- Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) ta shiga sahun jami'o'in tarayya da suka kara kudin makarantarsu
- Sabbin dalibai a tsangayar shari'a da ilimonin zamantakewa za su biya N151,200, yayin da tsoffin dalibai masu dawowa za su biya N89,200
- Haka kuma sabbin shiga a tsangayoyin da ke kwalejin kimiyar lafiya da tsangayar hada magunguna za su biya N190,200, inda dalibai masu dawowa za su biya N128,200
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Osun - Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), da ke Ife, a jihar Osun ta sanar da kari a kudin makarantarta.
Hukumar makarantar ta sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na makarantar, Abiodun Olarewaju.
Sabon kudin makarantar jami'ar OAU
Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya
Dalibai sabbin shiga a tsangayar shari'a da ilimonin zamantakewa za su biya Naira 151,200 yayin da tsoffin dalibai masu dawowa a tsangayar za su biya Naira 89,200.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sabbin dalibai a tsangayar kimiyya da fasaha za su biya Naira 163,200, inda tsoffin dalibai masu dawowa a tsangayar za su biya Naira 101, 200.
Bugu da kari, sabbin dalibai da suka samu gurbin karatu a kwalejin kimiyyar lafiya, da tsangayar hada magunguna za su biya Naira 190,200 sannan tsoffin dalibai masu dawowa za su biya Naira 128, 200.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an dauki matakin ne a taron gaggawa da majalisar dattawan jami'ar ta kira a ranar Talata, 12 ga watan Satumba.
Abun da daliban ke biya kafin karin kudin makarantar
Kafin karin, kudin makarantar OAU ya kasance N25,000 ga daliban tsangayar shari'a da ilimonin zamantakewa, yayin da daliban tsangayar kimiyya da fasaha, tsangayoyin da ke kwalejin kimiyyar lafiya da tsangayar hada magunguna ke biyan tsakanin N30,000 zuwa N40,000.
Ga sanarwar a kasa:
Daliban jami’ar Jos sun fantsama tituna don zanga-zanga kan karin kudin makaranta
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa daliban Jami’ar Jos da ke jihar Plateau sun bazama kan tituna don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta.
Daliban yanzu haka na zanga-zangar bijrewa karin kudin makarantar da ma sauran kudade da ake karba a makarantar.
Asali: Legit.ng