Binciken Gaskiya: Tinubu Na Shirin Daina Amfani Da Naira, a Koma Amfani Da Dala a Najeriya?

Binciken Gaskiya: Tinubu Na Shirin Daina Amfani Da Naira, a Koma Amfani Da Dala a Najeriya?

  • Wani bidiyo ya yaɗu a manhajar TikTok wanda ya nuna Shugaba Tinubu yana bayyana shirinsa na komawa amfani da dala a ƙasar nan
  • Sai dai, binciken diddigi da aka gudanar akan bidiyon ya bayyana cewa bidiyon ba ingantacce ba ne sauya shi aka yi
  • Tashar da aka jingina da fitar da bidiyon, Arise News ta fito ta nesanta kanta daga bidiyon inda ta ce na ƙarya ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyo da aka yaɗa a TikTok ya nuna shugaban ƙasa Bola Tinubu yana cewa yana shirin dai na amfani da naira ya koma amfani da dala a ƙasar nan.

Hukunci: Wannan batun ƙarya ne. Binciken Legit ya nuna cewa bidiyon sauya shi aka yi.

Gaskiyar batu kan shirin Tinubu na daina amfani da naira a koma dala
Wani bidiyon karya ya nuna cewa Shugaba Tinubu na shirin daina amfani da naira a koma dala a kasar nan Hoto: KOLA SULAIMON/AFP, LUDOVIC MARIN/POOL/AFP
Asali: Getty Images

Tinubu na shirin daina amfani da naira a koma dala?

Wani bidiyo da aka sanya a TikTok ya nuna mai gabatar da labarai a tashar Arise News, Ojy Okpe, tana gabatar da Shugaba Tinubu, wanda ya ce:

Kara karanta wannan

Malamar Da'awa Ta Fadi Cewa Ta Hango Peter Obi Ya Zama Shugaban Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna shirin daina amfani da naira sannan mu fara amfani da dala a matsayin kuɗin mu na gida."

Bidiyon wanda aka goge ya yaɗu sosai a manhajar inda kusan mutum 10,000 suka yaɗa shi sannan sama da mutum 2,000 suka yi sharhi a kansa a lokacin haɗa wannan rahoton.

Mutane da dama waɗanda suka kalli bidiyon sun yi amanna cewa ingantacce ne.

Wani mai amfani da sunan @erichbest a TikTok ya bayyana cewa:

"Wannan mutumin a hankali yana shirin sayar da ƙasar nan."

Sai dai, akwai waɗanda suka bayyana cewa bidiyon sauya shi aka yi.

Shin bidiyon ingantacce ne?

Legit ta bincika shafukan Arise News na yanar gizo, YouTube da Twitter amma ba ta samu bidiyon shugaban ƙasar yana bayyana hakan ba.

Legit ba ta kuma samu wata sanarwa wacce shugaban ƙasar ya yi ba kan shirin daina amfani da naira a koma dala.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Taɓarya Har Ya Mutu Kan Ƙaramin Abu

Idan aka lura da bidiyon sosai, za a fahimci cewa motsin leɓen Oke da Shugaba Tinubu bai yi daidai da abin da aka ji daga gare su ba. Wannan ya ƙara nuna cewa bidiyon an sauya shi.

Arise News ta nesanta kanta daga bidiyon

A halin da ake ciki, Arise News ta yi wani martani cikin wata sanarwa a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), inda ta ke cewa bidiyon ƙarya ne.

Sanarwar wacce Legit ta gani na cewa:

"ARISE News ta nesanta kanta daga bidiyon ƙaryan da ke yawo a soshiyal midiya yana ƙwaiƙwayon mai gabatar da shirin 'What's Trending' Ojy Okpe,"
"Bidiyon da aka sauya wanda ya yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin daina amfani da naira domin dala, aikin masu yaɗa labaran ƙarya ne."

Biden Ya Jinjinawa Tinubu

A wani labarin kuma, shugaban ƙasan Amurka, Joe Biden, ya yaba da kamun ludayin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaba Biden ya yaba da yadda Shugaba Tinubu yake gudanar da mulkinsa a Najeriya da shugabancin ƙungiyar ECOWAS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng