An Kama Fasto Bisa Zargin Dambarar Wata Mata Naira Miliyan 1.6 a Jihar Ondo
- Jami'an tsaron rundunar NSCDC sun damƙe wani Malamin addini bisa zargin zambatar wata mata kuɗi N1.67m a jihar Ondo
- Kakakin hukumar ya bayyana cewa Faston ya damfari wasu mutane da dama da ba a san yawansu ba a lokuta daban-daban
- Malamin cocin ya karɓi makudan kuɗin daga hannun matar da sunan zai taimaka mata ta sami biza cikin sauƙi
Jihar Ondo - Jami’an hukumar tsaron Sibil Difens ta Najeriya (NSCDC) sun kama wani malamin coci mai suna, Fasto Micheal Ogundepo, mai shekaru 39 a jihar Ondo bisa laifin zamba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ana zargin Malamin cocin, Ogundepo ya damfari wata wata mai suna, Misis Fagbuyiro Ajetomobi kudi har Naira miliyan 1.6.
Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar, Daniel Aidamenbor ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar a Akure, babban birnin jihar Edo.
Aidemenbor ya ce malamin da ake zargin ya kwace fasfo din Misis Ajetomobi kuma ya ci gaba da harkokin gabansa da kuɗinta wanda hakan ya hana ta sake neman wata takardar bizar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A jawabinsa, kakakin NSCDC ya ce:
"Mun kama Micheal Ogundepo, ɗan kimanin shekara 39, malamin coci mai lamba 15 a layin Ewu Agbo, Ikorodu Lagos bisa zargin damfarar Misis Fagbuyiro Ajetomobi Yemi da ke zaune a Akure."
"Faston ya zambaci matar ne da sunan zai taimaka mata ta samu Biza a kuɗi N1,670,000. Hukumar mu ta gayyaci wanda ake zargin amma ya ƙi amsa gayyata."
"Ya yi iƙirarin baya ƙasar nan kuma ya yi amfani da lambar ƙasar wajen ta ƙarya wajen kiran matar yana shirga mata ƙarya."
“An kama wanda ake zargin ne lokacin da aka gayyace shi ya karbi kudi N3,000,000 na aikin biza, ba tare da ya san cewa tarko aka ɗana masa ba."
Aidamenbor ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya damfari wasu abokan huldarsa da yawa waɗanda ba a san adadinsu ba, Vanguard ta rahoto.
Sanata Kalu Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da Labour Party a Kotun Zabe
Rahoto ya nuna cewa Sanata Kalu na jam'iyyar APC ya samu nasara kan PDP da Labour Party yayin da Kotun zaɓe ta yanke hukunci ranar Talata.
Kotun zaben NASS ta tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar Abia a matsayin halastaccen sanatan Abia ta arewa.
Asali: Legit.ng