Daliban Jami’ar Jos Sun Fantsama Tituna Don Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta

Daliban Jami’ar Jos Sun Fantsama Tituna Don Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta

  • Yayin da ake gasar karin kudin makaranta a jami’o’i, daliban Jami’ar Jos sun ce ba su amince da karin ba
  • A safiyar yau Talata 12 ga watan Satumba, daliban Jami’ar Jos su ka fito zanga-zanga don nuna damuwarsu a kai
  • Wannan na zuwa ne bayan Jami’o’i da dama sun kara kudin makaranta duba da halin da ake ciki a yanzu

Jihar Plateau – Daliban Jami’ar Jos da ke jihar Plateau sun bazama kan tituna don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

Daliban yanzu haka na zanga-zangar bijrewa karin kudin makarantar da ma sauran kudade da ake karba a makarantar.

Daliban jami'ar Jos na gudanar da zanga-zanga kan karin kudin makaranta
Daliban Jami’ar Jos Na Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta. Hoto: Joel Masha.
Asali: Facebook

Meye dalilin zanga-zangar na daliban?

Zanga-zangar ta samu jagorancin shugabannin dalibai inda su ka bukaci hukumomin makarantar su yi gaggawar sauya wannan mataki da su ka dauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

Daliban na dauke da kwalaye da ke nuni da rashin jin dadinsu da kuma korafi kan wannan lamari, Legit ta tattaro.

Kwalayen da dauke da sakwanni kamar haka: “Idan ‘ya’yanku za su iya biyan kudin, mu ba za mu iya ba.”, “Ba ma son barin karatu.” Da sauransu, Punch ta tattaro.

Meye Daliban ke cewa a Jos?

Daliban su ka ce halin da ‘yan kasar su ke ciki ma ya ishe su, don haka babu bukatar karin kuntatawa mutane a wannan lokaci.

Idan ba a manta ba, Jami'ar Jos da ke jihar Plateau ta kara kudin makarantar dalibai daga Naira dubu 45 zuwa dubu 213.

Magatakardar makarantar, Rejoice James Songden ita ta bayyana haka a ranar Juma'a 28 ga watan Yuli, Tori News ta tattaro.

Karin kudin makarantar akalla ya kai kaso 300 wanda daliban ke ganin ko kusa ba za su iya bayin wadannan kudaden ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kuma Kai Mummunan Farmaki Da Tsakar Dare, Sun Yi Ajalin Mutane 11, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Dole ce ta sa mu ka kara kudin makaranta a BUK, Farfesa Sagir

A labarin makamancin wannan, shugaban Jami'ar BUK, Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa dole ce ta saka su karin kudin makaranta a jami'ar.

Farfesan ya ce sun kara kudin ne ganin yadda farashin abubuwa su ka tashi wanda da su ake gudanar da jami'ar.

Ya ce matakin da su ka dauka shi ne dai-dai idan ba haka ba sai dai a rufe makarantar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.