Nyesom Wike: Daga Shiga Ofis, Sabon Ministan Abuja Ya Kama Ayyukan Tituna 135
- Nyesom Wike ya kaddamar da shirin gyare-gyare da facin hanyoyi da gwamnati za ta yi a Abuja
- Babban Ministan birnin tarayyan ya sanar da haka a lokacin da yake yi wa ‘yan kwangila kashedi
- Lokacin bada kwangila a Abuja, sai daga baya kudin aiki ya canza ya wuce a cewar sabon ministan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ministan birnin tarayya watau Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da ayyukan gyaran tituna 135 a garin Abuja a ranar Litinin.
Tun a ranar Asabar, Darektan yada labarai na ofishin Mai girma Minista, Anthony Ogunleye ya sanar da za a kaddamar da ayyukan a yau.
Premium Times ta ce wannan ya na cikin yunkurin sabuwar gwamnati wanda aka rantsar a karshen watan Mayu na ingana tituna a Abuja.
Ayyukan Nyesom Wike na farko a Abuja
Mista Ogunleye ya ce za a gudanar da ayyukan a unguwannin Garki, Wuse, Gwarimpa da Maitama, shi ne karon farko da za a fara yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a Ladoke Akintola Boulevard, Garki II, a Abuja, zai zama aikin abubuwan more rayuwan farko na ministan.
Ministan ya nuna jajircewarsa na tabbatar da gaggawan kawon cigaban abubuwan more rayuwa a babban birnin kasar."
- Anthony Ogunleye
Dazu rahoto ya fito daga Vanguard cewa Nyesom Wike ya gargadi ‘yan kwangila a kan yin sabani wajen tsaida kudin yin aiki a birnin na Abuja.
Wike ya yi bayanin ne a wajen bikin kaddamar da aikin titunan da ya bada wa’adin watanni shida, ya ce an yi hakan ne saboda kowa ya karasa aikin.
Babu maganar canza farashin aiki - Wike
"Game da ‘yan kwangila, bari in ja kunnenku yanzu. Duk wadannan abubuwan da ku ke yi da sashen injiniyoyi ba za su sake yin aiki ba.
Babu wani maganar canje-canje; ba zai yi aiki ba. Naira 1 ta dawo N15 bayan kwana 15, ba za ta sake aiki. Babu samun sabani a aikin nan."
- Anthony Ogunleye
Tsohon gwamnan ya ce su na da kudin da za su biya ‘yan kwangila, babu wanda zai bi gwamnati bashi, saboda haka dole su yi aiki a kan kari.
An gayyaci Ministoci a Majalisa
Kafin Ministocin Najeriya su yi wata guda a ofis, har ‘Yan majalisa sun fara aika masu goron gayyata, an kira Wale Edun, Dr. Doris Uzoka-Anite.
Kamar yadda rahoto ya zo kwanakin baya, gayyatar za ta ba Majalisa damar yin bincike da kyau a kan matsalolin tsare-tsaren zirga-zirga a kasar.
Asali: Legit.ng