An Kara Karyawa Tsagin Kwankwaso Ginshiki, Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP Daga Jihar Kano

An Kara Karyawa Tsagin Kwankwaso Ginshiki, Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP Daga Jihar Kano

  • An haramtawa dan tsagin Kwankwaso kujerar majalisar wakilai biyo bayan rashin gaskiya da ya aikata gabanin zaben majalisa
  • An ruwaito cewa, an ba dan takarar jam’iyyar APC kujerar bisa zuwa na biyu a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Ba a jihar Kano ba, an yi irin wannan a jihohi daban-daban na Najeriya a bana, inda aka kwace kujerun wasu ‘yan siyasa

Jihar Kano - Kotun sauraren kararrakin zabe ta Kano ta soke zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a majalisar wakilai.

Kotun dai ta danganta tsige dan majalisar wakilan na jam’iyyar NNPP ne bisa gaza yin murabus daga aikinsa a jami’ar Bayero ta Kano kwanaki 30 gabanin zaben, Daily Trust ta ruwaito.

Don haka mai shari’a Ngozi Azinge ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta ajiye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Datti a baya.

Kara karanta wannan

Ga ci ga rashi: An kwace kujerar sanatan PDP a Arewa, an ba wani fitaccen tsohon gwamnan APC

An tsige dan majalisar NNPP
Dan majalisar da aka tsige daga Kano kenan | Hoto: Datti Yusuf Umar
Asali: Facebook

Dan tsagin Ganduje a ba nasara

Hakazalika, kotun ta bayyana Musa Ilyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben a sahihance.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso ne na biyu mafi kuri’u a zaben da aka gudanar a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam na Majalisar Wakilai a ranar 25 ga Fabrairu 2023.

Ba a jiyar Kano kadai ba, an samu yanayi irin wannan a jihohi daban-daban na Najeriya saboda wasu matsaloli da aka gabatar a gaban kotun, Vanguard ta ruwaito.

An tsige dan majalisa a Imo

A bangare guda, an tsige dan majalisar wakilai na PDP a jihar Imo bayan da aka gano akwai kwane-kwane a zaben fidda gwani.

Hakazalika, an umarci gudanar da zaben a karo na biyu a wasu yankunan jihar Imo da ake kyautata zaton an samu tsaiko.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Kotu ta tsige fitaccen dan majalisar wakilai na PDP, ta fadi dalili

Sa’annan, an umarci INEC ta haramtawa dan majalisar ma suna Ikenga Ugochinyere shiga zaben da za a sake gudanarwa a jihar.

An tabbatar da zaben sanatan Legas

A wani labarin, kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Asabar ta tabbatar da Wasiu Eshinlokun-Sanni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Legas ta tsakiya.

Dan takarar jam’iyyar PDP Francis Gomez, ta bakin tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Joseph Daudu (SAN), ya koka kan wasu abubuwan yace jam’iyyar APC da dan takararta ba su samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.

Ya yi zargin cewa zaben ya kasance dauke da kura-kurai da cin hanci da rashawa, inda ya nemi kotu ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.