Tirkashi: An kori dan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC bayan ya zagi Sanata Danjuma Goje

Tirkashi: An kori dan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC bayan ya zagi Sanata Danjuma Goje

- Shugabancin jam'iyyar APC na gundumar Kumo ta gabas karkashin karamar hukumar Akko ta kori wani dan majalisar tarayya daga jam'iyyar

- Kamar yadda wasikar da aka aika ga ofishin jam'iyyar na kasa ta bayyana, an kama shi da laifin ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar

- An zargeshi da zagin Sanata Goje tare da aiko 'yan daba dauke da makamai inda suka hargitsa taron jam'iyya a Anguwan Akkoyel

Shugabannin jam'iyyar APC na karamar hukumar Akko ta jihar Gombe sun kori dan majalisar wakilai, Usman Kumo a kan zargin shi da ake da ayyukan zagon kasa ga jam'iyya.

Ana zargin Usman da raba jam'iyya tare da kokarin wargaza ofishin jam'iyya inda ya tura 'yan daba da makamai don hargitsa taron jam'iyya a Anguwan Akkoyel. Ya kara da zagi tare da tozarta shugaban jam'iyya, Sanata Danjuma Goje tare da yin kyauta mai tsoka ga wani tsagera da ya zazzagi sanatan.

Tirkashi: An kori dan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC bayan ya zagi Sanata Danjuma Goje

Tirkashi: An kori dan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC bayan ya zagi Sanata Danjuma Goje
Source: Facebook

Kamar yadda wasikar korar ta bayyana, an mika ta ne ga shugaban jam'iyyar APC ta kasa da ke titin Blant tyre a Wuse II, Abuja.

Wasikar ta bayyana cewa, "Bayan korafin da shugabannin APC na gundumar Kumo ta gabas da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe suka yi a kan Usman Bello Kumo, dan majalisa mai wakiltar Akko a tarayya, an zarge shi da

KU KARANTA: Babbar magana: Bidiyon yadda budurwa ta tona asirin Kwamishinan jihar Kogi da yayi mata fyade

1. Ayyukan zagon kasa ga jam'iyya.

2. Laifukan da za su iya zubar da kima, ci gaba da daidaituwar jam'iyya."

Kamar yadda wasikar ta ci gaba da bayyanawa, shugaban jam'iyyar na gunduma ya kafa kwamitin mutane bakwai wadanda suka yi bincike sannan suka mayar da rahoto bayan mako daya.

An gano cewa Usman Bello Kumo ya yi ayyukan zagon kasa a kan zaben Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya a 2019 wanda hakan ya ci karo da dokokin jam'iyya.

Ya aika an tarwatsa tare da lalata ofishin kamfen din jam'iyya da ke titin Bakoshi a Kumo.

Shine ya tura 'yan daba dauke da makamai inda suka hargitsa taron jam'iyya da aka yi a Anguwan Akkoyel.

Ya zaga tare da tozarta shugaba a jam'iyyar, Sanata Muhammad Danjuma Goje a wani shiri a gidan rediyon Kumo.

Ya yi wa wani Garba Inuwa Akoma Gona kyautar mota bayan ba daga mazabar shi yake ba kuma an gano cewa saboda zagin Sanata Goje ne da yayi.

Daga nan ne kuwa jam'iyyar ta yanke shawarar korar shi daga ranar 30 ga watan Maris 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel