Masu Garkuwa Da Mutane Sun Halaka Matar Aure a Gaban Mijinta a Jihar Taraba

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Halaka Matar Aure a Gaban Mijinta a Jihar Taraba

  • Miyagun ƴan bindiga da ake kyautata zatonasu garkuwa da mutane ne domin kuɗin fansa sun aikata ta'asa a jihar Taraba
  • Masu garkuwa da mutanen sun halaka wata matar aure tare da raunata mijinta bayan sun kutsa cikin gidansu da nufin sace su a birnin Jalingo
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa tana bakin ƙoƙarinta domin ganin miyagun sun shigo hannun hukuma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Taraba - Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun halaka wata matar aure tare da raunata mijinta a birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar tarho ga jaridar Daily Trust.

Yan bindiga sun halaka matar aure a Taraba
Yan bindiga sun halaka matar auren ne bayan sun je dauke su a jihar Taraba Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya auku

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankunan Da Za Su Ci Gajiyar Mulkin Shugaba Tinubu

SP Usman ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a unguwar Mil 6 ta cikin birnin Jalingo da safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Satumban 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun shiga gidan wani mai suna Mista Balanko Alex Gamalia inda suka harbe shi tare da matarsa a ƙoƙarinsu na sace shi.

Ya tabbatar da cewa matar Mista Salanko ta rasu a wajen, yayin da Mista Salanko wanda ya samu raunika ake duba lafiyarsa a asibiti.

Kakakin ya bayyana an sace mutum biyu ciki har da wata mata a gidan da ƴan bindigan suka kai hari.

Abdullahi ya ƙara da cewa ƴan sandan sun bi sahun masu garkuwa da mutanen inda ya buƙaci jama'a da su ba ƴan sanda bayanai waɗanda za su taimaka musu wurin gano miyagun da ke aikata laifuka a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ya Laƙume Rayukan Mutane Sama da 10 a Jihar Arewa

Ƙaruwar aikata laifuka a jihar Taraba na ci wa mutanen jihar tuwo a ƙwarya.

Ko a satin da ya gabata sai da wasu mutane suka biya kuɗin fansa har miliyan bakwai (N7m), kafin su samu ƴancinsu bayan an sace su.

Tsohon Shugaban PDP Ya Rasu

A wani labarin na daban, kun ji cewa Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Taraba, Cif Victor Bala Kona, ya riga mu gidan gaskiya.

Jigon na jam'iyyar PDP, ya mutu ne a safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Agustan 2023, a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng