An Hallaka Wata Mata a Wurin Taron Casu Yayin da Ta Tsaya Tsintar Kudi, an Yi Jana’izarta a Anambra

An Hallaka Wata Mata a Wurin Taron Casu Yayin da Ta Tsaya Tsintar Kudi, an Yi Jana’izarta a Anambra

  • An yi jana'izar wata 'yar jihar Anabmra da ake zargin ta kwashe kudade a wurin bikin da aka gayyace ta
  • An ruwaito yadda wasu tsageru suka hallaka wata budurwa bisa zargin ta yi sata, lamarin ya ba da mamaki
  • Ya zuwa yanzu, binciken 'yan sanda ya bayyana abin da ya faru, amma ahalin mamaciyar na bayyana shakku

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Anambra - An yi jana’izar wata ‘yar asalin jihar Anambra mai suna Chinyere Awuda, wacce aka tsinci gawarta a kusa da wani kududdufin wanka a harabar wani shahararren otal da ke Awka, Naija News ta ruwaito.

Matar mai shekaru 30 da haihuwa wacce ta kammala karatu a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, ta rasu ne a ranar 15 ga watan Yuli bayan an yi mata duka a otal kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kara karanta wannan

An kuma: Sanatan APC ya yi nasara kan PDP a gaban kotu, an yi watsi da duk wani zargi

An zargi Awuda da kwashe kudin da lika a lokacin bikin zagayowar ranar haihuwa, lamarin da ya sa wasu ’yan bani na iya suka yi mata dukan tsiya.

Yadda aka kashe budurwa ba bisa laifinta ba a Anambra
An yi jana'izar wata da aka kashe a Anambra | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jana’izar ta ya samu halartar tsoffin abokan makarantarta, kawayenta, da ‘yan uwa, wadanda suka bayyana ta a matsayin mace mai saukin kai da son jama’a, rahoton jaridar Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Iyayen marigayiyar, Mista da Mrs Awuda, wadanda suka kasa rike kukansu, sun koka da rasuwar ‘yarsu, inda suka ce bakin cikin su shi ne ‘yar tasu ta mutu “mutuwar da ba ta dace ba”.

Yadda ahalin marigayiyar ke kuka

Suka ce:

“Ita ce diyarmu ta biyar. Labarin mutuwarta ta zo mana cikin rudani. Ba mu taba tsammanin za a gajarta rayuwarta mai albarka da kyakkyawar makoma ba ta wannan hanyar ba.
“Mun samu labarin cewa wasu yara maza sun yi mata dukan tsiya har ta mutu, an kuma gano gawar ta a kusa da wani kududdufin wanka da aka daina amfani dashi a cikin otal din inda ta tafi tare da abokanta domin bikin zagayowar ranar haihuwar wani.

Kara karanta wannan

“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo

“Ko da yake ‘yan sanda sun ce binciken gawar ya tabbatar da cewa ta nutse ne, mun yi imanin an kashe ta ne saboda sun ki sakin faifan bidiyon CCTV na lamarin. Me za mu iya yi? Mun barwa Allah.”

Shima cikin bakin ciki, babban yayan marigayiyar, Ekene, ya koka da cewa ‘yan sanda da jami’an otal din ba su nuna tausayi ga ahalinsu ba.

Mata ta lakadawa miji duka

A wani labarin na daban, wata mata ta sumar da mijinta bayan ta lakada masa duka a layin Lambe Iluyomade a Ago Okota da ke cikin jihar Lagos.

Mutumin mai suna Edwin Ugwu dan shekara 56 ya labartawa kotun majistare a jihar Lagos yadda matarsa mai suna Ebere ta ke dukansa da zaran ya mata wani laifin da bai kai komai ba.

Miji ya ce irin azabtar dashi ta take ya yi yawa wanda har ya kai ga lakada masa dukan da ya suma aka wuce dashi asibiti, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.