Yadda aka lakada wa wani fasto bakin duka bayan ya caccaki shugaban karamar hukuma

Yadda aka lakada wa wani fasto bakin duka bayan ya caccaki shugaban karamar hukuma

Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wasu mutum 10 da ake zargi da sa hannunsu wajen lakada wa Fasto Okochi Chuwu Obeni mugun duka, bayan zarginsa da aka yi da sukar shugaban karamar hukumar a shafinsa na Facebook.

Sanarwar ta kara da cewa, jagoran wannan aika-aikar da ya shiga hannun 'yan sandan shine Julius Amadi Nyerere amma a halin yanzu ana ci gaba da bincike.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an ci zarafin Fasto Okochi Chuwu Obeni ne bayan da ya soki shugaban karamar hukumar Afikpo ta arewa, Ogbonnia Oko Eyim, a shafinsa na Facebook.

Ya zargi shugaban karamar hukumar da rushe gidan sirikansa da wasu shaguna tare da farfasa wata mota, BBC ta ruwaito.

Hakan ce ta sa Fasto Chuwu rubutu a Facebook inda yake cewa bai kamata ba abinda ya faru. Dole kowa yayi Allah-wa-dai dashi ba tare da duba wadanda abin zai bata wa rai ba.

Yadda aka lakada wa wani fasto bakin duka bayan ya caccaki shugaban karamar hukuma
Yadda aka lakada wa wani fasto bakin duka bayan ya caccaki shugaban karamar hukuma. Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: UGC

KU KARANTA: Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

Wannan al'amari kuwa ya matukar harzuka magoya bayan shugaban karamar hukumar har ta kai ga sun dauka mataki a hannunsu.

Wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuna yadda matasan suka daure Faston ta baya sannan suka dinga zabga masa bulala suna watsa masa ruwan kwata a kan idon jama'a.

Daga bisani suka tilasta masa janye kalaman da yayi.

A halin yanzu, yana asibiti saboda miyagun raunikan da aka ji masa kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A wani labari na daban, kwamitin yaki da muguwar cutar korona ta jihar Borno karkashin shugabancin mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, ya bayyana amincewarsa a kan yin sallar idi na wannan shekarar a jihar.

An kai ga wannan matsayar ne bayan Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada umarnin tuntubar Shehun Borno tare da yin taron malamai da limamai na jihar don samun matsaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng