Nyesom Wike Ya Musanta Gayyato EFCC, ICPC Su Binciki Magabacinsa Ministan Abuja

Nyesom Wike Ya Musanta Gayyato EFCC, ICPC Su Binciki Magabacinsa Ministan Abuja

  • Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa ya gayyaci EFCC, ICPC su binciki magabacinsa
  • Anthony Ogunlewe, darektan watsa labarai na ofishin ministan shi ne ya musanta rahotannin a cikin wata sanarwa
  • Ogunlewe ya ce tabbas akwai ayyukan da ministan bai gamsu da su ba wanda aka bayar da kwangilarsu a lokacin magabacinsa amma bai gayyato masa EFCC ko ICPC ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahoton da ke cewa yana shirin gayyatar EFCC da ICPC su binciki magabacinsa, Malam Muhammad Musa Bello, bisa aikata rashin daidai wajen bayar da kwangiloli.

A cikin wata sanarwa da darektan watsa labarai na ofishin ministan, Anthony Ogunlewe, ya fitar, ya bayyana cewa rahotannin zuƙi ta malle ce kawai babu ƙamshin gaskiya a cikinsu, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo

Wike ya musanta yi wa magabacinsa cinnen EFCC
Nyesom Wike ya musanta gayyato EFCC da ICPC domin bincikar magabacinsa ministan Abuja Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa Wike a lokacin duba ayyukan da ke cikin birnin tarayya, ya nuna damuwarsa da ɓacin ransa kan rashin daidai da ya lura da shi wajen yin wasu ayyukan da sauransu wanda ya bayyana hakan a bayyane.

Babu ƙamshin gaskiya a rahoton

Ogunlewe ya cigaba da cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bai taɓa tunani ko bayar da umarni ga wani daga ciki ko wajen ma'aikatarsa ya gayyato EFCC ko ICPC domin binciken tsohon ministan Abuja kan waɗannan abubuwan."
"Labarin yanar gizon da ake magana a kansa ba komai ba ne face ƙirƙirar mawallafansa wanda aka shirya domin kawo ruɗani a cikin al'umma."
"Muna kallon wannan labarin ƙaryan cike damuwa sannan muna kira ga al'umma da ƴan Najeriya nagari da su yi taka tsan-tsan da irin waɗannan rahotannin

Daga nan ya shawarci jama'a da su yi fatali da labarin gaba ɗayansa domin baya da tushe ballantana makama, rahoton Thisday ya tabbatar.

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Matashin Ango Ɗan Shekara 21 Ya 'Halaka' Amaryarsa Kan Rigimar Abinci

Ya ƙara da cewa Wike ya mayar da hankalinsa wajen yin aikin da ke gabansa yadda yakamata domin sauke nauyin da ke kansa cikin gaskiya.

Wike Ya Takali PDP Kan Hukuncin Kotu

A wani labarin na daban, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya takali jam'iyyar PDP kan rashin nasarar da ta yi a kotun zaɓe.

Ministan na birnin tarayya Abuja ya bayyana Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike ya ce bai san wa ya ba jam’iyyar PDP karfin halin tunanin nasara a kotun zaben shugaban kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng