“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo
- Matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Muhammad, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan wani mummunan al'amari da ya faru kwanan nan
- Hotunan ayarin motocinta da suka makale a ambaliyar ruwa a hanyarta ta zuwa kaddamar da wani cibiyar lafiya a jihar sun yadu
- Yayin da wasu suka alakanta halin da ta shiga da mugun shugabancin mijinta a jihar, wasu sun roki Allah ya shiga lamarin siyasar Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Bauchi - Ayarin motocin matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Muhammad, sun makale a cikin ambaliyar ruwa a hanyarsu ta zuwa tafiya.
Wani mai amfani da manhajar X Ainà Dipo @dipoaina1 ya tabbatar da lamarin a wata wallafa da ya yi a shafinsa tare da hotunan.
A cikin rubutun nasa wanda Legit.ng ta gano, ya alakanta halin da matar gwamnan Bauchin ta shiga da irin abun da ya faru da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.
A jawabin nasa, ya bayyana cewa "wannan zai fada maku abubuwa da dama cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da abun da take wakilta."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Allah ya kawo sauki," inji Dipo.
Yan Najeriya sun yi martani yayin da ayarin motocin matar gwamnan jihar Bauchi suka makale a tabo
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a game da lamarin bayan an wallafa shi a manhajar X wacce aka fi sani da Twitter a baya.
@Sunigab ya rubuta:
"Aikin mijinta ne. Kada ta yi mamaki."
@esin_kings32147 ya rubuta:
"Matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Muhammad a hanyarta ta zuwa Jamdan don kaddamar da wani cibiyar lafiya.
"Abun bakin ciki."
@munir__ell ya ce:
"Abun takaici idan babu hanya mai kyau da za a kai kayan asibiti da magunguna da kuma hanyar da garuruwan makwabta za su dunga zuwa cibiyar wannan wani abun kunya ne."
Mata 340 ne suka lakadawa mazajensu duka a jihar Lagas
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Lagas ta ce akwai karin rahotanni 340 na mata masu lakadawa mazajensu mugun duka a cikin shekara daya da ta gabata, Satumban 2022 da Yulin 2023.
Titilola Vivour-Adeniyi, shugabar hukumar yaki da cin zarafin mutane ta jihar Lagas, ce ta bayyana haka, jaridar PM News ta rahoto.
Asali: Legit.ng