Gwamnan Ribas Ya Saka Tukwicin N100m Kan Makashin DPO, Ya Dakatar Da Basarake Har Sai Baba Ta Gani

Gwamnan Ribas Ya Saka Tukwicin N100m Kan Makashin DPO, Ya Dakatar Da Basarake Har Sai Baba Ta Gani

  • Gwamna Fubara na jihar Ribas ya saka tukwicin naira miliyan 100 ga duk wanda ya kawo bayani da zai kai ga kama Gift David Okpara Okpolowu da mutanensa
  • Gwamnan ya dauki wannan matakin ne yayin da aka kashe DPO na yan sanda, SP Bako Angbashim a garin Osiemudie
  • Fabura ya kuma dakatar da basaraken yankin, Eze Cassidy Ikegbidi, har sai baba ta gani saboda hada kai wajen kyale guggun mutanen suna aikinsu cikin walwala a yankinsa

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya sanya tukwicin naira miliyan 100 kan wani mutum mai suna Gift David Okpara Okpolowu, wanda aka fi sani da 2-Baba da gaba daya mambobin kungiyarsa.

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, gwamnan jihar Ribas ya ayyana neman 2-Baba, da yan kungiyarsa kan kisan DPO, SP Bako Angbashim, a garin Odiemudie, karamar hukumar Ahoada ta gabas da ke jihar.

Kara karanta wannan

Cire tallafi: Shettima Zai rabawa talakawan jihohin Arewa 6 kayayyakin abinci

Gwamnan Ribas na neman makasan DPO
Gwamnan Ribas Ya Saka Tukwicin N100m Kan Makashin DPO, Ya Dakatar Da Basarake Har Sai Baba Ta Gani Hoto: @SimFubaraKSC, @RiversPoliceNG
Asali: Twitter

Gwamnan ya kuma dakatar da wani basarake, Eze Cassidy Ikegbidi, har sai baba ta gani saboda hada kai da shi wajen kisan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SP Bako Angbashim: Yadda aka kashe DPO a Ribas

A cewar sanarwar Gwamna Fubara, SP Bako , DPO na yankin Ahoada da tawagarsa sun shiga harin kautan bauna yayin da suke dawowa daga wajen aikinsu.

An harbi babban jami'in dan sandan yayin da aka bude wutar, inda maharan suka kama tare da kashe shi.

Gwamnan na jihar Ribas ya ce bayanan sirri daga hukumomin tsaro sun gano lamarin gaba daya yana da alaka da 2-Baba da guggun yan kungiyarsa.

Ya ce kungiyar ce ke da alhakin dawowar munanan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da ta’addanci a karamar hukumar Ahoada ta Gabas.

SP Bako Angbashim: Dalilin da yasa aka dakatar da basarake

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

Gwamna Fubara ya ce ya dakatar da Mai martaba, Eze Cassidy Ikegbidi Eze Igbu Akoh II, har sai baba ta gani saboda hada kai wajen barin guggun yan ta'addan suna aikinsu na ta'addanci cikin walwala a yankinsa.

“A matsayinmu na gwamnati da aka daurawa nauyi, ba za mu iya nade hannayenmu mu kyale masu laifi da masu aikata laifuka su tayar da munanan kawunansu da iko a kowani yanki na jiharmu ba," inji shi.

Fubara ya mika ta'aziyya ga iyalan SP Bako

Gwamna Fubara ya kuma aika sakon ta'aziyya ga iyalan SP Bako, musamman mata da yaransa da kuma rundunar yan sandan jihar.

Fubara ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar Ribas "ba za ta bari iyalinsa su wahala ba sakamakon rashinsa".

Yan Daba Sun Halaka DPO Na Yan Sanda a Jihar Rivers

A baya mun ji cewa yan bindiga da ake kyautata zaton ƴan daba ne, a ranar Juma'a da daddare sun halaka DPO na ƴan sanda a jihar Rivers, Bako Angbanshin.

Jaridar The Punch ta ce ƴan bindigan sun kama Angbanshin tare da yi masa gunduwa-gunduwa a ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel