Tinubu: Akwai Lokacin da Na Taba Aikin Gadi, Ilmi Ya Jawo Na Zama Shugaban Kasa
- Bola Ahmed Tinubu ya bada labarin zamansa mai gadi a shekarun baya kafin rayuwa ta yi masa kyau
- Shugaban Najeriyan ya ce ba komai ya taimaka masa ya samu gyadar doguwa ba illa ilmin zamaninsa
- Mai girma Tinubu ya zauna da ‘Yan Najeriya da ke zaune a kasar Indiya, ya ba su wasu 'yan shawarwari
Abuja - A ranar Alhamis, Bola Ahmed Tinubu, ya ce an yi lokacin da yake yin aikin gadi, amma yau ya zama shugaban kasar Najeriya.
A lokacin da ya zauna da ‘yan kasarsa da ke zaune a Indiya, Ajuri Ngelale ya fitar da jawabin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai da hulda da jama’a ya ce mai gidansa ya yi bayanin yadda ilmi ya taimaka masa.
Bola Tinubu wanda ya ke halartar taron G-20 ya ba daliban Najeriya da ke karatu a kasashen Asiya su maida hankali a wajen samun ilmi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jawabin Bola Tinubu a Indiya
"Ilmi mai kyau ya kawo ni nan kuma ina farin ciki da na ke tsayawa a gabanku a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Na fara sannu a hankali ne. Na yi mai gadi. Na yi malami a makaranta. Ina da basira a lokacin ina dalibin makaranta.
Na shiga Deloitte kuma na samu horaswa a daya daga cikin mafi girman kamfanonin akanta a duniya saboda ilmi na."
- Bola Tinubu
Yadda Bola Tinubu ya samu nasara
Mai girma Bola Tinubu yake bada labarin zuwansa kamfanin Exxon Mobil da yadda ya shiga harkar siyasa domin ya kawo gyara.
Vanguard ta ce shugaban ya kwadaitar da masu ci-rani a Indiya su bada gudumuwa a Najeriya.
"Lokacin da na fara aiki da su, na tambaye su: ‘Ku na da rassa a Najeriya?’, su ka ce ‘Mu na da abokan hulda da yawa za su karbe ka idan ka tafi gida.
A haka na tafi kamfanin Exxon Mobil kuma na zama fitaccen akanta, babban mai binciken kudi kuma ma’aji kafin shiga siyasa."
- Bola Tinubu
Gudumar Shugaban Najeriya Tinubu
Daga lokacin da Bola Tinubu ya karbi mulki, Bisoye Coker-Odusote ta canji Aliyu Abubakar Aziz yayin da aka tura shi ritayar dole a NIMC.
Janar Babagana Monguno ya rasa mukaminsa na NSA tare da sauran hafsun sojoji kamar yadda shugaban kasa ya kori shugaban NASENI.
Asali: Legit.ng