Yan Daba Sun Halaka DPO Na Yan Sanda a Jihar Rivers

Yan Daba Sun Halaka DPO Na Yan Sanda a Jihar Rivers

  • Miyagun ƴan bindiga da ake zargin ƴan daba ne sun salwantar da DPO na ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar Rivers
  • Bako Angbanshin ya rasa ransa ne bayan ƴan daban sun yi masa kwanton ɓauna tare da jami'ansa lokacin da suka fita neman miyagu
  • Ƴan daban sun yi gunduwa-gunduwa da gawar Angbanshin bawan sun cafke shi lokacin da harsashin jami'ansa ya ƙare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Rivers - Ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan daba ne, a ranar Juma'a da daddare sun halaka DPO na ƴan sanda a jihar Rivers, Bako Angbanshin.

Jaridar The Punch ta ce ƴan bindigan sun kama Angbanshin tare da yi masa gunduwa-gunduwa a ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas da ke jihar.

Yan daba sun halaka DPO a jihar Rivers
Yan daban sun yi wa jami'an yan sandan kwanton bauna ne Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Miyagun sun yi masa kwanton ɓauna yayin da ya fita aiki da sauran jami'an ƴan sanda, domin kai sumame a maɓoyar masu aikata laifi a Ahoada ta Gabas.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

Yadda lamarin ya auku

A cewar wani majiya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ƴan daban suna ɗauke da miyagun bindigu guda huɗu inda suna ganin jami'an tsaron kawai suka buɗe musu wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An yi musayar wuta na kusan mintuna bakwai a tsakanin tawagar DPO da tawagar 2Baba ta ƴan daban Iceland, har zuwa lokacin da harsashin jami'an tsaron ya ƙare." A cewarsa.

Majiyar ya bayyana cewa yayin da sauran ƴan sanda suka janye bayan sun hango rashin nasara, Angbanshin bai bar wajen ba.

An tattaro cewa lokacin da Angbanshin ya yi ƙoƙarin barin wajen, ya samu karaya inda ƴan daban suka kama shi da ransa suka yi awon gaba da shi.

Sai dai, wani bidiyo da ya yaɗu a ranar Juma'a da daddare, ya nuna kan Angbanshin, hannu da al'aurarsa an raba su da gangar jikinsa.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Saki Hamɓararren Shugaban Kasar Ali Bongo, Sun Fadi Dalili

A cikin bidiyon, ƴan daban sun yi ta rera waƙoƙin samun nasara yayin da gawar Angbanshin take kwance a ƙasa.

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar Rivers, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da halaka DPO ɗin, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

"Eh da gaske ne, zan bayar da cikakkun bayanai ranar Asabar (yau) da safe."

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 a Benue

A wani labarin na daban, ƴan bindiga da aƙe kyautata zaton ƴan fashin daji ne sun halaka mutum uku a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.

Daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka halaka a ƙauyen Ugba na ƙaramar.hukumar ta Logo, har da jami'an tsaron ƙungiyar 'yan sakai ta jihar Benue State Volunteer Guards (BSCVG).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng