Jerin Nasarori 7 da Gwamnatin Bola Tinubu Ta Samu Cikin ‘Yan Kwanaki a Indiya

Jerin Nasarori 7 da Gwamnatin Bola Tinubu Ta Samu Cikin ‘Yan Kwanaki a Indiya

  • Bola Ahmed Tinubu ya na kasar Indiya inda ake yin taron ‘Yan G20 da sauran kasashen Duniya
  • Shugaban kasar ya na sa ran kamfanonin waje za su shigo da hannun jari domin bunkasa tattalin arziki
  • Tun lokacin kamfe, Tinubu ya yi alkawari gwamnatinsa za ta samar da ayyukan yi domin matasan kasar

Abuja - A wannan rahoto na musamman, Legit.ng Hausa ta bibiyi zuwan da Bola Tinubu ya yi Indiya, ta kawo muhimmancin ziyayar.

Mista Olusegun Dada, ya na cikin hadimin shugaban kasa, ya fara sanar da wadannan albishir a shafin X a safiyar Alhamis dinnan.

Tinubu
Nasarorin zuwan Bola Tinubu Indiya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

1. ‘Yan kasuwan Indiya

Manyan ‘yan kasuwan kasar Indiya sun gamsu su zo Najeriya domin yin kasuwanci, attajiran za su zuba hannun jarin Dala biliyan $14bn

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wike: Abokin Fadan Atiku Ya Yi Wa PDP Shakiyanci a Kan Shari'ar Zaben 2023

2. Kamfanonin karafuna

Kamfanin Jindal Steel and Power Ltd da ke birnin New Delhi a Indiya ya yi alkawarin kashe $3bn domin a rika sarrafa karafuna a nan.

3. Aikin wutar lantarki

Bayanai sun tabbatar da kamfanin SkipperSeil Limited zai samar da tashohin wuta har 20 masu kafin megawatt 100 nan da shekaru hudu.

4. MoU

Bosun Tijjani wanda ya na cikin tawagar ya yi bayanin yarjejeniya da aka shiga tsakanin Najeriya da Indiya a bangarorin da za su amfanar.

5. Harkar noma

Kamfanin Indoroma ya yarda zai batar da $8bn wajen kafa kamfanin da zai fadada samar da takin zamani, sanarwar ta ce za a gina kamfanin a Ribas.

6. Sha’anin tsaro

Daga yanzu zuwa 2027, ‘yan kasuwar Indiya sun sha alwashin kashe $1bn a kan hukumar DICON, hakan zai bunkasa aikin sojoji da kuma na tsaro.

7. Wasu yarjejeniyar $800m

A sakamakon ziyarar ne fadar shugaban kasa ta ce Bharti Enterprises za su batar da $700m a kasar nan a fannin inshora, abinci, gidaje da sauransu.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Kotu Ta Daure Matashi Shekaru Dubu 11 A Gidan Kaso Kan Zargin Damfara Na Crypto, Ta Yi Bayani

Wike: Karfin halin PDP

Idan aka koma siyasa, za a ji labari Nyesom Wike ya ce abin da shari’ar zaben 2023 ta kunsa dabam da hayaniyar da ake yi dandalin sada zumunta.

Duk da ya na ‘dan jam’iyyar PDP, Ministan birnin na Abuja ya karbi mukami a hannun gwamnatin APC, hakan ya fusata 'ya 'yan jam'iyyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng