Auren Zawarawan Kano: Sheikh Aminu Daurawa Ya Ce Za a Yi Kade-kade Da Musulunci Ya Amince Da Su
- Sheikh Aminu Daurawa, ya yi magana kan auren zawarawan da gwamnatin Kano za ta gudanar
- Ya ce za a yi kaɗe-kaɗe irin wanda Musulunci bai hana a yi su ba cikin shagulgulan bikin
- Sai dai Daurawa ya ce ba za su bar kowa ya shiga da waya wurin shagalin ba don kar a ɗauki matan mutane hoto
Kano - Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa suna kan shirye-shiryen yadda za a gudanar da auren zawarawan da gwamnatin jihar Kano ta shirya yi.
Daurawa ya bayyana cewa za a yi kaɗe-kaɗe irin waɗanda addinin Musulunci bai hana ba a wajen shagalin bikin kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Daurawa ya fadi irin kaɗe-kaɗen da za a yi a wajen auren zawarawa
Sheikh Aminu Daurawa wanda shi ne babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayani kan shirye-shiryen hidimar da ke ƙaratowa.
Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar Kano dai ta shirya tsaf, domin aurar da zawarawa da 'yan mata 1800 a duka ƙanan hukumomin jihar 44.
Daurawa ya bayyana cewa za a yi kaɗe-kaɗe irin na ƙwarya da na shantu wajen nishaɗantar da zawarawa da 'yan matan da za a aurar.
Ba ma iya masu kidan kwarya da na shantu ba, Daurawa ya ce za a yi nau'ikan shagulgula daban-daban domin nishaɗantar da amaren.
Dubu 500 aka warewa kowace karamar hukuma
Daurawa ya ci gaba da cewa a cikin tsare-tsaren da suka gudanar, sun warewa kowace ƙaramar hukuma naira 500,000 domin gudanar da shagulgulan.
Legit.ng a kwanakin baya ta kawo rahoto kan yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ware kudi sama da miliyan 800 domin gudanar da auren na zawarawa a jihar.
Sheikh Aminu Daurawa a wani jawabi da ya yi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa auren wani shiri ne da gwamnanti ta zo da shi don ƙara inganta walwalar 'yan jihar.
Abba ya ware miliyan 700 don biyan kuɗin makarantan ɗaliban BUK
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan naira miliyan 700 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ware, don biyawa ɗaliban da ke karatu a jami'ar Bayero 'yan asalin jihar Kano kuɗin makaranta.
Hakan wani ƙoƙari ne da gwamnan ke yi wajen ganin ya ragewa ɗaliba da iyayensu raɗaɗin matsin rayuwar da suke ciki.
Asali: Legit.ng