"Jamiyyar PDP Ce Uwa Ga Dukkan Jam'iyyu A Najeriya", Atiku Ya Bayyana Matsayin PDP
- Jigon jamiyyar PDP kuma tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka kan hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe
- Atiku ya ce jam'iyyar PDP ita ce uwar ko wace jamiyya a Najeriya har ma da jamiyyar APC mai mulki da sauransu
- Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 7 ga watan Satumba a Abuja yayin martani kan hukuncin kotu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi alfaharin cewa jamiyyar PDP ita ce uwar ko wace jamiyyar a Najeriya.
Atiku ya bayyana haka ne a yau Alhamis 7 ga watan Satumba a Abuja yayin martani kan hukuncin kotu.
Meye Atiku ya ce kan PDP?
Tsohon shugaban kasar na magana ne yayin da ya ke martani kan hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce jamiyyar PDP ita ce uwar ko wace jamiyya a Najeriya har ma da jam'iyyar APC mai mulki.
Ya bukaci mambobin jamiyyar da su kasance masu hakuri da kuma biyayya ga jam'iyyar.
Ya kara da cewa jamiyyar PDP ita ta haifi mutane da dama har ma da wadanda ba su da kishi da su ka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu, Premium Times ta tattaro.
Ya ce:
"Bari na karawa wasu mambobinmu kwarin gwiwa wadanda ba su ji dadi ba.
"Ni na kasance farkon wadanda su ka kafa jam'iyyar PDP kuma har yanzu ina da karfi na.
"Wannar jam'iyya ita ta haifi dukkan sauran jam'iyyu, ko kana APC ko APM da sauransu."
Wane shawara Atiku ya bai wa mambobin PDP?
Atiku ya ce abu mafi muhimmanci shi ne mu zama masu hakuri da biyayya ga jamiyyar PDP inda ya ce ita kadai ce tsohuwar jamiyyar tun 1999 zuwa yau, cewar Vanguard.
Hukuncin Kotun Zabe: Shettima Ya Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo, Ya Ce Zai Siya Masa Kaji Da Akuyoyi Ya Fara Kiwo
Ya kara da cewa:
"Ya kamata mu kare ta tare da ingantata, za ka iya zama uba yau amma dole ka tuna da kakanka ko kakan kakanka.
"Ban ga dalilin da ya sa ba za ka yi alfahari da kasancewa dan jam'iyyar PDP ba."
Atiku ya bukaci mambobin jamiyyar da su kasance masu hakuri da kuma juriya don ciyar da jamiyyar gaba.
Atiku Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya yi martani kan hukuncin kotun zabe.
Atiku ya ce bai yadda da hukuncin ba kuma zai daukaka kara zuwa kotun koli don kwato musu hakkinsu.
Asali: Legit.ng