Shugaba Tinubu Ya Mika Sakon Ta'aziya Ga Iyalan Marigayi Sheikh Giro Argungu
- Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwarsa kan babban rashi da aka yi na shahararren malamin addinin Musulunci
- Tinubu ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ba ga iyalansa ba har ma da kasa baki daya ganin irin gudummawar da ya bayar
- Marigayi Sheikh Giro Argungu ya rasu a jiya Laraba 6 ga watan Satumba a garin Argungu da ke jihar Kebbi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tura sakon jaje ga iyalan marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu.
Sheikh Giro ya rasu a jiya Laraba 6 ga watan Satumba a garin Argungu da ke jihar Kebbi.
Wane sako Tinubu ya tura ga iyalan Sheikh Giro?
Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 63 bayan fama da jinya a garin Argungu da ke jihar Kebbi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ya tura sakon jajen ne a yau Alhamis 7 ga watan Satumba inda ya bayyana rasuwar marigayin da babban gibi.
Shugaban ya bayyana ta'aziyar ce ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale a shafin Twitter na fadar shugaban kasa.
Shugaban ya ce mutuwar Giro babbar asara ce ganin yadda ya ba da gudunmawa a bangaren addini da kuma tarbiyya.
Ya bayyana rashin Giro ba iya 'yan uwansa ko yankinsa ba ne, gaba daya Najeriya sun yi babban rashi.
Tinubu ya bayyana gudumawar da Giro ya bayar
Sanarwar ta ce:
"Ba za a taba mantawa da muryar Giro ba na tsawon lokaci wurin aiki ga addinin Musulunci da kuma tarbiyya.
"Ayyukan malamin musamman kasancewarsa a kungiyar Izalah ta JIBWIS ya sauya zukatan matasa da dama."
Tinubu ya ce rashin marigayin ba karamar asara ba ce ganin yadda malamin ya ke gudanar da wa'azinshi ba tare da tsoro ba.
Ya kuma mika ta'aziya ga iyalan mamacin da gwamnatin jihar Kebbi da al'ummar Musulmi baki daya, PM News ta tattaro.
Sheikh Giro Argungu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
A wani labarin, Allah ya karbi rayuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu a jiya Laraba 6 ga watan Satumba bayan fama da jinya.
Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Bala Lau shi ya sanar da rasuwar malamin a jiya Laraba 6 ga watan Satumba a shafinsa na Facebook.
Asali: Legit.ng