Jerin Alkalan Kotun Koli Da Za Su Yanke Hukunci A Karshe Bayan Sanin Sakamakon Kotu A Jiya
FCT, Abuja - Bayan hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa, jam'iyyar PDP da Labour sun kudiri aniyar daukaka kara.
A watan Maris, hukumar zabe ta sanar Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour, Peter Obi sun kalubalanci zaben da aka gudanar.
A jiya Laraba kotun ta yi fatali da korafe-korafensu da cewa ba su da gamsassun hujjoji.
'Yan takarar sun sha alwashin daukaka kara a gaba zuwa kotun koli don kwatar hakkinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng ta jero muku alkalan kotun koli kara da za su yanke hukunci a gaba.
1. Shugaban Alkalan Najeriya (CJN), Olukayode Ariwoola
Hukuncin Kotun Zabe: Shettima Ya Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo, Ya Ce Zai Siya Masa Kaji Da Akuyoyi Ya Fara Kiwo
An zabi Olukayode Ariwoola a matsayin alkalin kotun koli a shekarar 2011.
ICIR ta tattaro cewa Ariwoola ya wakilci tsohon shugaban alkalan Najeriya, Tanko Muhammad da su ka wargaza zaben jam'iyyar APC na jihar Zamfara.
2. Musa Dattijo
An zabe Musa Dattijo alkalin kotun koli a shekarar 2012.
Kafin wannan lokaci ya rike matsayin shugaban alkalan jihar Niger a 1989.
3. Kudirat Motonmori Olatokunbo
An zabi Kudirat a matsayin alkaliyar kotun koli a ranar 8 ga watan Yuni na 2013.
Ita ta karanto hukuncin da ya rusa karar Emeka Ihedioha na jihar Imo a 2020.
4. John Inyang Okoro
Inyang ya samu karin girma zuwa kotun koli a ranar 15 ga watan Nuwamba 2013.
5. Chima Centus Nweze
Chima Centus ya zama alkalin kotun koli a 2014 bayan aiki a kotun daukaka kara tsakanin 2008 zuwa 2014.
6. Amina Adamu Augie
Amina ta samu shiga kotun daukaka kara a 2002 da kuma zuwa kotun koli a 2016.
7. Uwani Musa Abba Aji
Uwani ta shiga kotun koli a watan Janairu na shekarar 2019.
Ta na daga cikin alkalan da su ka rusa zaben jamiyyar APC a jihar Zamfara a 2019.
8. Mohammed Lawal Garba
Garba ya samu shiga kotun koli a ranar 6 ga watan Nuwamba 2016.
Ya na daga cikin alkalan da su ka tabbatar da Ahmed Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben Yobe ta Arewa a majalisar Dattawa.
9. Helen Moronkeji Ogunwumiju
Helen Moronkeji ta shiga kotun koli a ranar 6 ga watan Nuwamba 2020.
Ita ma ta na daga cikin alkalan da su ka tabbatar da Ahmed Lawan a matsayin wanda ya lashe zabe.
10. Ibrahim Musa Saulawa
Saulawa ya samu shiga kotun koli a ranar 10 ga watan Nuwamba 2020.
Kafin wannan lokaci Saulawa ya shiga jerin alkalan kotun daukaka kara a watan Yuni na 2016.
11. Adamu Jauro
Jauro na daga cikin alkalai takwas da su ka samu karin girma zuwa kotun koli a shekarar 2020.
12. Emmanuel A. Agim
Agim ya shiga jerin alkalan kotun koli a shekarar 2020.
Kafin wannan lokaci, Agim shi ne shugaban alkalan kasar Gambia da kuma shugaban kotun koli a Swaziland.
13. Tijjani Abubakar
Abubakar na daga cikin wadanda su ka samu shiga kotun daukaka kara a 2020 da majalisar alkalai ta tabbatar da su.
Kotu Ta Yanke Hukuncin Zaben Shugaban Kasa
A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke hukunci kan shari'ar da ake yi.
'Yan takarar jam'iyyun PDP da Labour na kalubalantar zaben da cewa an tafka magudi.
Asali: Legit.ng