Akalla Mutane 6 Ne Su Ka Rasa Rayukansu Sakamakon Hatsarin Mota A Jihar Ondo

Akalla Mutane 6 Ne Su Ka Rasa Rayukansu Sakamakon Hatsarin Mota A Jihar Ondo

  • Jimami yayin da hatsarin mota ya rutsa da wasu mutane har guda shida a kan hanyar Akure da ke jihar Ondo
  • Kwamandan Hukumar FRSC a jihar, Ezekiel Sonallah shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Laraba
  • Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na rana inda ya ce an rasa rayukan mutane shida yayin hatsarin motar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Hukumar Kula da Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da cewa akalla mutane shida sun rasa rayukansu dalilin hatsarin mota.

Hatsarin motar ya faru ne a kan hanyar Akure zuwa Owo da ke jihar Ondo da misalin karfe 1:00 na rana a yau Laraba 6 ga watan Satumba.

Hatsarin mota ya kashe mutane 6 a jihar Ondo
Hukumar FRSC ta sanar da mutuwar mutane 6 sakamakon hatsari a jihar Ondo. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Meye ya jawo hatsarin motar a Ondo?

Kwamandan hukumar a jihar, Ezekiel Sonallah shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Laraba 6 ga watan Satumba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Shari'ar Tinubu Da Obi: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Yadda Ubangiji Zai Turo Wakili Kan Shari'ar Zabe, Ya Bayyana Mai Nasara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sonallah ya ce hatsarin ya rutsa da babbar motar daukar mai da kuma wata karamar mota kirar Toyota Sienna.

Ya kara da cewa karamar motar fasinja kirar Toyota Sienna din na dauke da fasinjoji takwas inda mutum daya ya samu raunuka a jikinsa.

Sonallah ya ce an samu wayoyin hannu da kuma kudade wanda hukumar ta mika su ofishin jami’an ‘yan sanda da ke Ogbese.

FRSC ta bai wa direbobi shawara don kiyaye hatsari

Yayin da ya ce an dauki gawarwakin mutane shidan zuwa babban asibiti da ke Akure babban birnin jihar Ondo, Vanguard ta tattaro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ka’ida da kuma shan kai ba bisa ka’ida ba da ya jawo gagara gudanar da motocin.

Ya ce:

“Ina rokon direbobin motoci da su rinka bin ka’aidar tuki musamman abin da ya shafi yawan gudu.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

“Direbobin motocin kasuwa ya kamata su tabbatar sun saka na’aurar kiyaye yawan gudu da kuma kula a ko wane lokaci.”

Ya shawarci direbobin har ila yau, da kada su wuce mutum ba tare da kula da abin da ke nufo su ba.

Hatsarin Mota Ya Sanadin Wasu Fasinjoji 6 a Jihar Oyo

A wani labarin, akalla mutum shida sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu mutum 14 suka samu raunika, a hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Ibadan-Oyo a karamar hukumar Afijio ta jihar Oyo.

Shaidun gani da ido sun tabbatar cewa direban wata farar mota kirar Toyota Hummer mai daukar fasinjoji 18 ce motar ta kwace masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.