Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Fallasa Masu Satar Man Fetur a Najeriya

Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Fallasa Masu Satar Man Fetur a Najeriya

  • Majalisar wakilai ta shirya tsaf domin fallasa ɓarayin da ke sace man fetur da iskar gas a ƙasar nan
  • Shugaban kwamitin majalisar mai bincike kan satar man fetur din, Kabiru Rurum, shi ne ya tabbatar da hakan
  • Rurum ya bayar da tabbacin cewa kwamitin ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya magance matsalar satar man fetur a ƙasar nan

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar wakilai mai binciken satar man fetur da raguwar kuɗaɗen shiga daga iskar gas, ya sha alwashin fallasa waɗanda ke da hannu wajen satar man fetur a Najeriya.

Jaridar Daily Trust tace Kabiru Rurum, shugaban kwamitin shi ne ya bayyana hakan kafin fara zaman kwamitin da aka shirya a ranar 7 ga watan Satumba.

Majalisar wakilai za ta fallasa sunayen barayin man fetur
Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa sashen shi ne babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa kwamitin a shirye yake wajen ganin cewa ya yi abin da ya dace saɓanin waɗanda aka kafa a baya.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

A cewarsa satar man fetur na cigaba da ƙamari a ƙasar nan wanda hakan ke janyo babbar asara wajen kuɗaden shigar da ƙasar nan ke samu, rahoton The Guardian ya tabbatar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Maƙasudin kafa kwamitin shi ne fallasa masu hannu kan abin da ke faruwa a ɓangaren satar man fetur." A cewarsa.

A daina ɗorawa jami'an tsaro laifi

Rurum ya bayyana cewa ɗora alhakin satar man fetur ɗin kan jami'an tsaro ba zai wadatar ba, inda ya ƙara da cewa duk wasu masu ruwa da tsaki a ɓangaren mai irinsu Chevron, Shell, da ƙauyukan da ake samun man fetur ɗin, na da abun faɗa kan satar man da ake yi.

"Muna buƙatar gano masu hannu a ciki, wannan shi ne maƙasudin gudanar da binciken. Duk wasu masu ruwa da tsaki a ɓangaren za su zo su gaya mana abin da suka sani dangane da lamarin." A cewar Rurum.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Reshen Jihar Kano Ta Sanar Da Sabbin Matakan Da Ɗauka

Ya bayyana cewa masu ruwa da tsakin za su bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen dakatarwa ko rage satar ɗanyen man fetur ɗin wanda dama hakan shi ne babban maƙasudin kafa kwamitin.

Peter Obi Ya Yi Nasara Kan Tinubu a Kotu

A wani labarin na daban, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya samu nasarar a kan Shugaba Tinubu a kotun zaɓen shugaban ƙasa.

Kotun ta ƙi amincewa da buƙatar APC da Tinubu ta ƙalubalantar kasancewar Peter Obi mamban jam'iyyar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng