Peter Obi Ya Yi Nasara Kan Shugaba Tinubu Da Kashim Shettima a Kotun Zabe

Peter Obi Ya Yi Nasara Kan Shugaba Tinubu Da Kashim Shettima a Kotun Zabe

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ƙi amincewa da ƙorafe-ƙorafe guda biyu da APC da Tinubu suka shigar akan Peter Obi
  • APC da Tinubu sun ƙalubalanci zaman Peter Obi mamba a jam'iyyar Labour Party da cancantar ƙararsa bisa rashin yon haɗaka da Atiku Abubakar
  • Kotun a yayin yanke hukuncinta ta ƙi amincewa da ƙorafe-ƙorafen guda biyu da APC da Tinubu suka shigar a kan Peter Obi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi nasara akan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Peter Obi ya samu nasara a kansu ne akan wasu ƙorafe-ƙorafe guda biyu kan takararsa da kuma ƙarar da ya shigar, cewar rahoton PM News.

Peter Obi ya yi nasara kan Tinubu a kotu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ƙorafi na farko shi ne a kan zaman Peter Obi mamba a jam'iyyar Labour Party sannan na biyun shi ne, ko ƙarar da ya shigar ta cancanta saboda bai yi haɗaka da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ba, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Babban Sanatan Jam'iyyar APC, Ta Bayyana Dalilanta

APC da Bola Tinubu a cikin ƙararsu sun yi ƙorafin cewa babu sunan Peter Obi a cikin jerin sunayen mambobin jam'iyyar Labour Party da aka ba INEC a ranar 25 ga watan Afirilun 2022, wanda hakan ya saɓawa sashe na 77 na sabuwar dokar zaɓe ta 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hukunci kotun ta yanke?

Ɗaga cikin alƙalan kotun guda biyar, mai shari'a Abba Mohammed, wanda ya karanto hukuncin kotun kan ƙarar, ya ƙi amincewa da ƙorafin Tinubu da Shettima kan ƙalubalantar zaman Peter Obi ɗan jam'iyyar Labour Party.

"Jam'iyya ce kaɗai za ta iya bayyana mambobinta, sanann babu wani mahaluƙi da zai yi bincike a kai." A cewar alƙalin.

Kotun ta kuma ƙi amincewa da ƙorafin masu shigar da ƙara na cewa Peter Obi bai yi haɗaka da Atiku Abubakar ba wanda ya zo na biyu a zaɓen, wajen shigar da ƙararsa.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Malamin Addini Ya Fadawa Alkalai Abinda Ya Kamata Su Yi

Alƙalin ya ce mai shigar da ƙara bai zama tilas dai ya yi haɗaka da wani ɗan takara wanda ya yi rashin nasara kamarsa ba a wajen shigar ƙararsa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Ya bayyana cewa ya zama tilas ne kawai mai shigar da ƙara ya sanya sunan wanda ya ci zaɓe da jam'iyyarsa da hukumar da ta shirya zaɓen a matsayin waɗanda ke cikin ƙarar da ya shigar.

Kotu Ta Kori Karar Peter Obi Kan Tinubu

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yo fatali da ƙarar da Peter Obi ya shigar kan zargin Shugaba Tinubu da safarar miyagun ƙwayoyi.

Kotun ta yi watsi da ƙarar inda ta ce Peter Obi da jam'iyyarsa sun kasa kawo gamsassun hujjoji a gabanta kan zargin Shugaba Tinubu da safarar ƙwayoyi a Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng