Shugaba Tinubu Ya Sauka a Indiya, Ya Gana da Fitaccen Attajirin Ƙasar
- Bola Ahmed Tinubu ya isa ƙasar Indiya domin halartar taron G20, ya gana da shugaban rukunin kamfanonin Hinduja Group
- Shugaban ƙasar ya ce ƙofar Najeriya a buɗe take wajen zuba hannun jari wanda zai samar da ayyukan yi a karkashin gwamnatinsa
- A nasa ɓangaren, fitaccen Attajirin, Prakash Hinduja, ya ce ya shirya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Najeriya
New Delhi, India - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa New Delhi, babban birnin kasar Indiya domin ziyarar aiki ta kwanaki shida, inda zai halarci taron shugabannin kasashen G20.
Tinubu ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Indira Gandhi da ke Delhi tare da wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministoci da hadiman shugaban kasa.
Shugaba Tinubu ya gana da Attajirin Indiya
Jim kaɗan isarsa, Tinubu ya gana da Mista Prakash Hinduja, shugaban rukunin kamfanonin Hinduja Group kuma babban Attajiri.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayanai sun nuna cewa fitaccen Atttajirin ya mallaki dukiyar da a ƙiyasi ta haura Dala biliyan 100.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa, inda ya ce ganawar mutanen biyu ta fara ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
Abinda suka tattauna a taron
A sanarwan, wacce hadimin shugaban ƙasa ya wallafa a manhajar X, shugaba Tinubu ya ce
"Mun shirya tsaf domin kasuwanci. Na zo nan da kaina don tabbatar wa abokanmu da masu zuba jari cewa babu wani cikas da ba zan karya na kawar da shi ba."
"Najeriya za ta zama daya daga cikin wurare masu kyau a duniya na samun riba mai kyau da samar da ayyukan yi masu dorewa.”
"Da goyon bayana, babu wani abu da zai hana ku jin daɗin damarmakin da babbar kasuwarmu take da su da kuma hazaka da ƙwazon 'yan Najeriya. Ƙofar kasuwancin mu a bude take."
A nasa bangaren, shugaban kamfanonin Hinduja ya faɗa wa Tinubu cewa shi shaida ne kan kokarin da ya yi a lokacin yana gwamnan jihar Legas.
Ya ce a shirye yake ya zuba hannun jari a Najeriya da kuma rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu.
Majalisar Dokokin Oyo Ta Amince Wa Gwamna Ya Karbo Bashin N50bn
A wani labarin kuma Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo zai karɓo bashin kuɗi Naira biliyan 50 domin gudanar da harkokin gwamnatinsa.
Wannan ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi wa buƙatar a zamanta na ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2023.
Asali: Legit.ng