Juyin Mulki: Shugaban Ƙasar Guinea Bissau Ya Kara Wa Masu Tsaronsa Karfi
- Shugaba Umaro Embalo na ƙasar Guinea-Bissau ya naɗa sabbin jami'ai a tawagar masu gadin shugaban ƙasa yayin da juyin mulki ke yaɗuwa a Afirka
- A 2022, wasu sojoji sun yi yunkurin yi wa shugaban ƙasar Guinea Bissau juyin mulki amma ba su samu nasara ba
- Da yake jawabi, Embalo ya ce za a ɗauki mataki kan duk wani motsi da ke da ayar tambaya
Guinea-Bissau - Shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo, ya ƙara naɗa karin jami'ai biyu domin ƙara ƙarfafa tsaronsa yayin da juyin mulki ya zama ruwan dare a Nahiyar Afirka.
Channels tv ta tattaro cewa shugaban ƙasar ya naɗa sabbin dogaran ne domin ƙara tsaurara matakan tsaro a kewayensa, yana mai ishara da abinda ke wakana a Afirka.
Shugaba Embolo ya yi wannan sabbin naɗi ne biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar da kuma Gabon, wanda duka jami'an tsaron gwamnati ne suka aiwatar.
Embolo ya amince da naɗin Janar Tomas Djassi a matsayin shugaban dakarun tsaron shugaban ƙasa da kuma Janar Horta Inta a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban ƙasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wadannan mukamai guda biyu sun dade a cikin tsarin gwamnatin ƙasar Guinea Bissau amma tsawon shekaru masu yawa ba a naɗa kowa ba.
An rantsar da Djassi da Inta a ranar Litinin a wani kwarya-kwaryan biki da aka shirya a fadar shugaban kasa, kamar yadda wani dan jaridar AFP ya bayyana.
Tarihin juyin mulki a ƙasar Guinea-Bissau
Kasar Guinea-Bissau dai ta sha fama da juyin mulkin soji har sau hudu tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1974, na baya bayan nan ya faru a shekarar 2012.
Haka nan kuma an yi yunƙurin kifar da gwamnatin Embalo a watan Fabrairu na shekarar da ta gabata 2022.
"Gaskiya ne juyin mulkin da masu gadin fadar shugaban kasa ke yi ya zama abin burgewa," in ji shugaba Embolo yayin da yake hira da manema labarai a ranar Litinin.
Ya kuma tabbatar da cewa duk wani motsi da ba a yarda da shi ba, za a ɗauki mataki nan take.
Kafin sabon nadin nasa, Djassi ya kasance shugaban masu gadin kasa, wani fitaccen rukunin sojoji, wanda kawo ɗaukinsa ya taimaka wajen dakile yunkurin juyin mulkin 2022.
Juyin Mulki ko Kashe Shi: Malamin Najeriyan da Ya Gano Abin da Zai Faru da Bazoum
A wani rahoton kuma Wani malamin musulunci, Najeriya, Aliyu Ibrahim Kaduna ya yi magana kwanaki game da abin da yanzu ya faru a Jamhuriyyar Nijar.
An yi hira da Shugaba Mohammed Bazoum, aka ji yana cewa Nijar za ta fara buga kudinta, ta daina dogaro da Faransa da ta mallake su a baya.
Asali: Legit.ng