Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ofisoshin Gwamnati Da Sauran Cibiyoyi a Kano

Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Rufe Ofisoshin Gwamnati Da Sauran Cibiyoyi a Kano

  • Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Kano, ta bi sahun uwar kungiya ta kasa
  • Ƙungiyar ta sanar da rufe ofisoshin gwamnati da duk wasu manyan ma'aikatu da ke faɗin jihar
  • Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne domin cika umarnin uwar ƙungiya ta ƙasa na tsunduma yajin aikin kwanaki biyu na gargadi

Kano - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Kano, ta shiga yajin aikin gargaɗi da ake gudanarwa a faɗin kasar, ta hanyar rufe ofisoshin gwamnati da sauran cibiyoyi a jihar.

A rahoton jaridar Vanguard, an bayyana cewa tun da sanyin asubahin ranar Talata ne dai jami'an ƙungiyar suka fito domin tabbatar da cika umarnin uwar kungiya ta ƙasa.

NLC reshen jihar Kano ka ta bi sahun uwar kungiya ta kasa
Kungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Kano ta rufe ofisoshin gwamnati. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ƙungiyar ƙwadago ta rufe ofisoshin gwamnati a Kano

Mataimakin shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Ado Riruwai, a zantawarsa da manema labarai, ya bayyana cewa yanzu haka sun rufe duk wasu ofisoshin gwamnati da ke jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 18 da Suka Lashe Zaɓe a Jiharsa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Riruwai wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masana'antu ma su zaman kansu, ya ƙara da cewa ma'aikatar samar da wutar lantarki da kuma bankuna ma za su kasance a rufe.

Ya kuma bayyana cewa za su je har filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano domin tabbatar da cewa babu wani jirgi da aka bari ya tashi.

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa dai ta tsunduma yajin aikin na gargaɗi ne domin nunawa gwamnati halin ƙuncin da ake ciki a yanzu.

Wani rahoto na BBC ya bayyana cewa rufe bankuna zai yi matuƙar shafar harkokin hada-hadar tattalin arziƙin ƙasa.

TUC ta fice daga yajin aikin kungiyar kwadago

A wani labarin mai alaƙa da wannan da Legit.ng ta wallafa a baya, kungiyar 'yan kasuwa ta TUC, ta ce ba za ta shiga yajin aikin gargaɗi da kungiyar ƙwadago ta shirya gudanarwa ba.

Kara karanta wannan

Shugabannin Ƙungiyar NLC Sun Kunyata Ministan Tinubu, Sun Fatali da Taron FG

Shugaban kungiyar TUC Festus Osifo, a cikin jawabin da ya gabatar, ya bukaci kungiyar ta ƙwadago ta ƙasa da ta ci gaba da tattaunawa da gwamnati don samun abinda ake so.

Tun a makon da ya gabata ne dai kungiyar ƙwadagon ta sanar da cewa za ta tsunduma yakin aiki na gargaɗi a ranar Talata, 5 ga watan Satumba.

Tinubu ya koka kan yawan ma'aikata da ke cinye kuɗaɗen ƙasa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan damuwar da Shugaba Bola Tinubu ya nuna kan yawan ma'aikatan gwamnati da ke karɓar albashi a matakan jihohi da na tarayya.

Tinubu ya bayyana cewa hankalinsa na matuƙar tashi a duk lokacin da ya ga tulin ma'aikatan da ake biya albashi a duka matakai na gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng