Yan Sanda Sun Ceto Mutum 3 Da Bindiga Suka Sace a Jihar Kaduna

Yan Sanda Sun Ceto Mutum 3 Da Bindiga Suka Sace a Jihar Kaduna

  • Ƴan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu bayan jami'an ƴan sanda sun ritsa su a ɗaji a jihar Kaduna
  • Jami'an ƴan sandan sun fatattaki ƴan bindiga sannan suka samu nasarar ceto mutum uku da suka yi garkuwa da su a Zariya
  • Jami'an tsaro na ƙara matsa ƙaimi wajen ganin sun kakkaɓe miyagun ƴan bindiga da suka daɗe suna addabar mutane

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Jami'an ƴan sanda a jihar Kaduna sun ceto mutum uku da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan sun fita wani sintiri a yankunan Kuriga da Wusasa cikin Zariya, cewar rahoton Channels tv.

Yan sanda sun ceto mutum 3 da yan bindiga suka sace a Kaduna
Yan sandan sun ceto mutanen ne bayan sun fita sintiri Hoto: @NigeriaPoliceForce
Asali: Facebook

Muƙaddashin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Manir Hassan, shi ne ya tabbatar da ceto mutanen daga hannun miyagun ƴan bindigan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Tarzoma a Kasa, Ta Magantu Kan Masu Hannu a Ciki

Yadda aka ceto mutanen

ASP Manir ya bayyana cewa jami'an ƴan sanda sun ceto mutanen ne bayan wani sintiri da suka fito a yankunan Kuriga da Wusasa na Zariya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa an samu nasarar ceto mutanen ne ta hanyar haɗin gwiwa da ƴan sakai, waɗanda suka samu bayanan sirrri kan motsin ƴan bindigan.

Kakakin ya cigaba da cewa bayan samun bayanan sirrin sai tawagar jami'an tsaron ta shiga dajin wanda hakan ya tilasta ƴan bindigan guduwa cikin daji suka bar mutanen.

Ya yi bayanin cewa ana zargin yaran gawurtaccen ɗan bindigar nan Isah Danwasa, ɗan asalin Zariya, su ne suka yi garkuwa da mutanen.

Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Jere

Ƴan bindiga sun kai farmaki a garin Jere na ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna. Ƴan bindigan sun halaka mutum biyu a yayin farmakin da suka kai cikin tsakar dare.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah Da Sace Mutane Masu Yawa

Ƴan bindigan waɗanda suka yo gayya ɗauke da muggan makamai sun kuma yi awon gaba da mutum 11 a yayin harin.

Uba Sani Ya Umarci a Gudanar Da Bincike

A wani labarin da muka kawo muku kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayar da umarnin yin bincike kan harin da ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Saya-Saya na jihar.

Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen ne inda suka halaka wasu bayin Allah lokacin da su ke yin Sallar Isha'i a ƙauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng