Matsalar Cire Tallafin Mai Da Abubuwa 2 Da Tinubu Ke Fama Da Su A Mulkinsa Bayan Cika Kwanaki 100
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na fama da wasu matsaloli da ya gada a tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.
A ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Tinubu ya sanar da cire tallafin mai wanda ya zamo babbar matsala ga jam’iyya mai mulki ta APC wanda ba su yi tsammani ba.
Wannan matsalar na karuwa ganin yadda har zuwa yau ba a shawo kanta ba duk da shafe watanni uku a kan mulki.
Duk da cewa shugaban ya sha alwashin cika alkawuran da ya dauka, amma matsaloli sun dabaibaye shi da su ka hada da matsalar tattalin arziki da rashin tsaro da kuma karyewar darajar Naira.
Legit.ng ta jero muku wasu manyan matsaloli guda uku da wannan gwamnati ke fama da su watanni uku kenan a kan mulki:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Kudaden rage radadin cire tallafi
Cire tallafin mai da shugaban ya yi ya jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali da tsadar abinci wanda ba a taba gani ba.
Ganin yadda ake cikin wannan hali, Tinubu ya sanar da ba da Naira biliyan biyar ga ko wace jihaa don tallafawa mutane.
Hakan bai rage komai ba inda ‘yan kasar ke kukan cewa a dawo da tallafi don talaka ya samu sauki.
2. Kungiyar Kwadago ta NLC
Daga cikin manyan matsalolin da Tinubu ke fuskanta shi ne matsayarsa da kungiyar NLC.
Kungiyar ta bukaci Tinubu ya kara mafi karancin albashi daga dubu 30 zuwa dubu 150 ko 200, amma masana na cewa hakan zai yi wahala ganin yadda kasar ke fama da tattalin arziki.
3. Juyin mulki a Nijar da Gabon
Shugaba Tinubu na gudanar da abubuwa biyu a kasarshi, shi ne shugaban kasar Najeriya kuma a lokaci guda shugaban kungiyar ECOWAS.
Tinubu bai kammala shawo kan matsalar Nijar ba, sai ga shi an sake juyin mulki a Gabon.
Tinubu ya bayyana cewa ya tsorata da halin da ake ciki a Gabon yayin da ya ke kokarin shawo kan matsalar Nijar duk da sojin kasar sun ce ba za su mika mulki nan kusa ba.
Nijar: Tinubu Ya Ce Shi Ya Ke Takawa Dakarun ECOWAS Birki
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya ce shi ya ke takawa dakarun ECOWAS birki kan afkawa kasar Nijar.
Ya ce idan da ba don shi ba, da tuni dakarun sun afkawa kasar da yaki don kwato mulki daga hannun sojoji.
Asali: Legit.ng