Ambaliyar Ruwa a Jihar Kebbi Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 3
- Ambaliyar ruwa da aka yi garin Dakingari ta yi sanadin mutuwar mutane aƙalla uku
- An bayyana cewa ruwan sama da aka shafe sa'o'i da dama ana yi ne ya janyo ambaliyar ruwan
- Gwamnati ta shawarci mazauna yankin da su guji yin gine-gine a kan hanyoyin ruwa da kuma zubar da shara barkatai
Kebbi - Mutane aƙalla uku ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta wakana a Dakingari da ke ƙaramar hukumar Sulu ta jihar Kebbi.
Shugaban ƙaramar hukumar Sulu Alhaji Muhammad Lawal Suru ne ya bayyana hakan kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.
Yadda ambaliya ta janyo mutuwar mutane 3 a Kebbi
Lawal ya bayyana cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, sakamakon mamakon ruwan da aka shafe sa'o'i masu yawa ana yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce ruwan da ya riƙa gangarowa daga kan tsaunukan da ke zagaye da garin na Dakingari ne ya ƙara taimakawa wajen ƙaruwar ambaliyar.
Ya ƙara da cewa sun shafe sama da shekara 20 suna fama da matsalar ambaliyar, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatocin Nasamu Dakingari da ta Atiku Bagudu suka yi na maganceta.
Yadda za a magance matsalar ambaliyar ruwan
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa za a iya magance matsalar ta hanyar gina shinge na kankare da kuma hanyoyin fitar ruwa a jikin tsaunukan da ke gangaro da ruwan.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su guji yin gine-gine a kan hanyoyin ruwa da kuma zuba shara da sauran tarkace a cikin magudanan da ruwa ke wucewa.
Ya ƙara da cewa sun bai wa waɗanda abin ya shafa tallafi, sun kuma sanar da gwamnatin jihar da sauran hukumomi domin kawo mu su ɗauki.
Jaridar The Cable a kwanakin baya ta yi rahoto kan matakan da jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara suka ɗauka na dakile faruwar ambaliyar ruwa a garuruwansu.
Ruwa sama ya lalata sama da gidaje 100 a Kebbi
Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan gidaje sama da 100 da kuma tarin dukiya da ruwan sama mai haɗe da iska ya lalata a jihar Kebbi.
Hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA), reshen jihar ta Kebbi ce ta bayyana hakan, inda ta shawarci mazauna karkara da birane da su koyi ɗabi'ar dashen itatuwa don rage tasirin iska.
Asali: Legit.ng