Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuwar Soji da wasu Mutane 9 a jihar Kebbi

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuwar Soji da wasu Mutane 9 a jihar Kebbi

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da tabbacin salwantar rayukan wani soja da kuma wasu Mutane 9 sakamakon aukuwa 2 ta ambaliyar ruwa a yankuna daban-daban dake fadin jihar.

Cikin wata sanarwa da sanadin Abubakar Dakingari, mai magana da yawun gwamnan jihar, Alhaji Atiku Bagudu, shine ya bayyana hakan da cewar ambaliyar ruwan ta auku cikin wasu kananan hukumomi biyu na jihar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Ambaliyar ta auku cikin kauyen Kanya dake karamar hukumar Danko Wasagu da kuma kauyen Mahuta dake karamar hukumar Fakai, inda tuni gwamnan jihar ya kai ma su ziyarar jajantawa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu an tsamo gawarwaki takwas da suka riga mu gidan gaskiya inda ake ci gaba da kai komo wajen laluben sauran da ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar katse ma su hanzari.

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuwar Soji da wasu Mutane 9 a jihar Kebbi
Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuwar Soji da wasu Mutane 9 a jihar Kebbi
Asali: Facebook

Legit.ng ta fahimci cewa, ruwan dare wanda hausawa kan ce mai game duniya shine ya yi sanadiyar ambaliyar ruwa a kauyukan da ta rusa gidaje da dama, gonaki da kuma salwantar dabobi kamar yadda mai garin Kanya, Alhaji Isah Dan Hassan ya shaidawa gwamnan yayin ziyarar sa.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu garkuwa Mutane 3 a jihar Kano

A sanadiyar haka Alhaji Dan Hassan ya nemi gwamnatin jihar akan ta gina gadaje da kuma kwale-kwale na kwana-kwana domin jiran tsammanin aukuwar wannan annoba a lokuta na gaba.

A nasa bangaren shugaban karamar hukumar Fakai, Musa Jarma, ya bayyana cewa akwai kimanin gidaje 48 da aukuwar wannan annoba ta salwantar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel