FIRS Ta Tara Makudan Kudi, Gwamnoni da Tinubu Za Su Raba Naira Tiriliyan 3.8

FIRS Ta Tara Makudan Kudi, Gwamnoni da Tinubu Za Su Raba Naira Tiriliyan 3.8

  • Asusun gwamnatin Najeriya ya cika taf da harajin hatimi da bankuna su ke karba a kasar nan
  • Lokaci ya yi da za a raba kudin da aka samu tsakanin gwamnatoci da wadanda su ke da hakki
  • Kwararrun da su ka taimaka aka samu kudin shigan su na da kaso a wannan tiriliyan 3.8

Abuja - Bayanai sun fito a game da yadda za ayi rabon Naira Tirilyan 3.8 da gwamnatin Najeriya ta samu daga harajin hatimi.

Gwamnatocin jihohi da kuma gwamnatin tarayya su ne za su tashi da kaso mafi tsoka na tiriliyoyin a cewar jaridar nan This Day.

Adadin abin da za a raba shi ne N3,860,867,322,987.42 inda gwamnonin Najeriya kadai za su karbi 73% na kudin shigan da aka tara.

Tinubu
Bola Ahmed Tinubu (GCFR) da Shugabannin NESG Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Abin da kowa zai samu a kudin

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Jero Dabarun da Za Ta Bi Domin Gyara Tattalin Arzikin Najeriya

Gwamnatin tarayya za ta samu 14% daga cikin kudin yayin hukumar FIRS mai alhakin tattara haraji a kasar nan za ta samu 4%.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwararrun da su ka yi sanadiyyar samun kudin su na da 5% na Naira tiriliyan 5%, amma ba za a sake biyansu a cikin kason ba.

Rahoton ya ce lauyoyin gwamnatin tarayya su na da 2% yayin da bankuna da wasu za su samu 2% da za a biya sau daya a tashin farko.

Gwamnatocin tarayya da na jihohi za su cigaba da karbar kudin a duk lokacin da aka tara harajin da a jawo aka shigar da kara a kotu.

Rikicin Malami v Wike

A lokacin ya na ministan shari’a kuma lauyan gwamnati, Abubakar Malami SAN ya je kotu a kan rikicin yadda za ayi rabon kudin.

Nyesom Wike a sa’ilin bai zama ministan Abuja ba, ya kalubalanci hurumin gwamnatin tarayya wajen karbar haraji a jihohi.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Tinubu Ya Nemo Hanyar Sauki, Zai Samar Da Sabbin Gidajen Mai 9,000 Madadin Na Fetur, Bayanai Sun Fito

A karshe aka sasanta ba tare da an je kotun koli ba, amma har Muhammadu Buhari da gwamnonin su ka bar ofis, ba a raba kudin ba.

Wata majiya ta ce gwamnonin jihohin kasar nan sun tsorata da yadda bankin CBN yake cigaba da rike harajin da aka karba a bankuna.

Tinubu zai je taron G20

Rahoto ya zo cewa Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya na cikin Ministocin tarayya da za su raka Bola Tinubu zuwa taron G20 a Indiya.

Tawagar shugaban Najeriya ta na dauke da Ministan harkokin kasashen waje, Amb. Yusuf Tuggar, Dr. Doris Uzoka-Anite da Bosun Tijani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng