Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Da Sace Wasu Mutum 11 a Jihar Kaduna
- Ƴan bindiga sun salwantar da rayukan mutum biyu a wani hari da suka kai a garin Jere na jihar Kaduna
- Ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum 11 a garin ciki har da ma'aikata masu aiki a wani gidan biredi
- Mazauna garin sun koka kan rashin ɗaukin da jami'an tsaro suka ƙi kai musu duk da kiran gaggawa da aka yi musu
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun halaka mutum biyu tare da sace mutum bakwai masu aiki a gidan biredi da wasu ƴan haya mutum huɗu a Unguwar Kwanan Pete ta garin Jere na jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ce wani mazaunin Jere, Hamisu Yahaya, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Talata da misalin ƙarfe 9:40 na dare.
Yadda lamarin ya auku
Ya bayyana sunayen waɗanda ƴan bindigan suka halaka a matsayin Mai Unguwa Alhaji Aliyu da Akilu, wani mai yin achaɓa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa ƴan bindigan waɗanda suka yo gayya ɗauke da makamai, sun farmaki gidan biredin Albarka inda suka sace ma'aikata bakwai, sannan suka shiga wani gida kusa da gidan biredin suka sace mutum huɗu.
A cewarsa marigayi Alhaji Aliyu, wanda ya ji motsin da bai gamsu da shi ba sai ya fito domin ganin abin da ke faruwa, sai kawai ɗaya daga cikin ƴan bindigan ya harbe shi.
Ƴa bayyana cewa ɗayan mamacin wanda ɗan achaɓa ne, yana kan babur ɗinsa lokacin da suka buɗe masa wuta inda ya rasu nan take a wajen.
"Sun kwashe kusan sa'a ɗaya suna cin karensu babu babbaka, amma babu jami'an soja ko ƴan sanda da suka kawo ɗauki kan kiran gaggawa da aka yi musu, duk da ƙarar harbe-harben bindigar da suka cika garin Jere a wannan daren." A cewarsa.
Abin da hukumomi suka ce kan harin
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige, kan sace mutanen har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Sai dai, sakataren masarautar Jere, Alhaji Aliyu Zubairu, ya tabbatar da sace mutum 11 da halaka wasu mutum biyu a yankin.
Uba San Ya Bayar Da Umarnin Bincike
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ƙaduna, Malam Uba Sani ya ba jami'an ƴan sanda umarnin su gudanar da bincike kan harin da aka kai a ƙauyen Saya-Saya na ƙaramar hukumar Ikara ta jihar.
Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne bayan ƴan bindiga sun buɗe wuta kan wasu masallata a ƙauyen bayan sun kai wani farmaki.
Asali: Legit.ng