Rundunar Yan Sanda Ta Kaddamar Da Bincike Kan Zargin Mata Masu Shan Jini a Kano
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi martani a kan rade-radin da ake yi na bullar wasu mata masu jan jini a jihar
- Kakakin rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce suna kan bincike a kan al'amarin
- Hakazalika, rundunar yan sandan Bauchi ta karyata rahotannin cewa mata masu shan jini sun bulla a jihar tare da shanye jinin al'umma
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Hukumar yan sandan jihar Kano ta sanar da fara gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa wasu mata masu shiga gidan mutane suna shanye masu jini.
Jaridar Aminiya ta rahoto cewa an samu bullar wani bidiyo da ke yawo a yan baya-bayan nan wanda ya nuna yadda ake dukan wasu mata kan zargin cewa masu shan jini ne.
Hakazalika, akwai wasu hotuna da suka dunga yawo na wata mata wacce aka damke a karamar hukumar Gazawa bayan an zarge ta da shan jinin wata matar gidan.
Da aka nemi jin ta bakinsa kan wannan al'amari, kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa sun kaddamar da bincike a kan al'amarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Koda dai bai tabbatar da gaskiyar al'amarin ba, Kiyawa ya ce suna kan gudanar da bincike.
Da aka nemi karin bayani kan ko an kai musu rahotannin faruwar irin wannan batu, sai ya ce “muna gudanar da bincike” kawai.
Ba gaskiya bane rahoton mata masu shan jini a Bauchi, Rundunar yan sanda
A wani labari makamancin wannan, rundunar yan sandan jihar Bauchi ta yi watsi da rade-radin cewa wasu mata na shiga gidajen mutane suna shanye masu jini.
Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum
Kafar labarai ta TRT ta rahoto cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya karyata labarin da ke ta yawo a soshiyal midiya cewa wasu mutane 20 da ake zargin suna da maita sun shiga jihar tare da shan jinin al'umma.
Ya kuma karyata wani bidiyo da ya dunga yawo a soshiyal midiya na wata mata da aka yi zargin tana da maita, inda ya ce sam ba haka abun yake ba.
SP Wakil ya ce:
“Sunan matar Siddika, kuma mazauniyar Unguwar Shekal ce, ta tafi wata unguwa mai suna Bakin Kura a garin Bauchi domin neman sadaka, sai ta fadi saboda yunwa.
“Ana haka ne wasu mata da matasa suka fara jifanta da duwatsu, suna mai cewa mayya ce."
Sakamakon bincike ya nuna matar na da tabin hankali
Har ila yau, ya bayyana cewa ko da suka samu labarin afkuwar lamarin, sai Kwamishinan yan sandan Bauchi, CP Auwwal Musa Mohammad ya bada da umarni ceto matar cikin gaggawa.
Ya ci gaba da cewa:
“Binciken da muka gudanar ya nuna matar tana da lalurar tabin-hankali amma ba mayya ba ce kuma mun mika ta hannunyan uwanta."
Rundunar yan sandan ta kuma ja hankalin al'umma da su daina yada jita-jita ko abun da basu da tabbaci a kansa.
Mutum 6 sun riga mu gidan gaskiya a wani hatsarin mota a jihar Osun
A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Osun, ta bayyana cewa mutum shida sun rasa ransu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Imesi-Ile.
Kwamamdan hukumar, Mista Henry Benamesia, shi ne ya bayyana hakan ta hannun kakakin hukumar Mrs Agnes Ogungbemi, a birnin Osogbo, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumban 2023.
Asali: Legit.ng