Budurwa ta gwangwaje kanta da motar naira miliyan 26, jama'a sun tofa albarkacin bakinsu

Budurwa ta gwangwaje kanta da motar naira miliyan 26, jama'a sun tofa albarkacin bakinsu

- Wata matashiya ta gwangwaje kanta da kyauta ta musamman a ranar masoya wacce ta yi rijistar sunan ta a cikin kungiyar masu motoci

- Ta je shafin sada zumunta na Twitter domin nuna kayatacciyar mota kirar Audi da ta siyawa kanta a daren ranar masoya

- Masu amfani da shafukan sada zumuntar sun jinjina mata saboda irin dandano da take da shi na zabar motar ta miliyan 26

Wata budurwa ta cika da farin ciki saboda ta sami sabon matsayi yanzu. Yarinyar ta nuna hadaddiyar abar hawan da ta mallakawa kanta a shafin ta na Tuwita a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu.

@QueenGifti yayin wallafa wani hoto na hadaddiyar motar tare da makulinta ta bayyana kanta a matsayin mamba a tawagar masu Audi.

Motar da ta siyawa kanta ba irin abar hawa da aka saba gani na yau da kullun ba ce. Audi A7 ce wacce farashin ta ya kai kimanin $ 69,200 (N26 miliyan), a cewar Car Buzz.

Budurwa ta gwangwaje kanta da motar naira miliyan 26, jama'a sun tofa albarkacin bakinsu
Budurwa ta gwangwaje kanta da motar naira miliyan 26, jama'a sun tofa albarkacin bakinsu Hoto: @QueenGifti
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu

Kyautar tata ta haifar da cece-kuce a shafin Twitter, inda tuni wallafan ya samu sama da like guda 54,000 da kuma martani masu yawa.

Masoyan mota sun yaba da zaɓinta na kyakkyawar abar hawa, wasu kuma sun yi mata maraba da shiga 'ƙungiyar Audi.'

@shy_rots:

"Mota mai kyau, Na mallaki 2018 A4 na shekara biyu, na siyar da ita watanni 3 da suka gabata .. kyakkyawar mota."

@carlrossautos ya ce:

"Muna taya ki murnar mallakar sabuwar abar hawa.

"Da Audi, kin samu fitilu mafi kyau a cikin unguwarku.

“Kira na musamman aka yi wa Audi.”

"Mallaki Audi a yau.

"Tawagar Audi ita ce bam."

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Tsohon Shugaban kasa ya yi martani a kan tashin hankalin da ke kasar

A wani labarin, Yan Najeriya sun kwararawa wata budurwa sakonnin taya murna ga kyakkyawar budurwa yar Arewa bisa nasaran da ta samu.

Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi sanarwa a shafin Tuwita bisa kammala karatun digirinta a fannin karatun lauya.

Maryam, wacce bata bayyana jami'ar da ta kammala ba ta godewa Allah bisa nasarar da ta samu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel