Dan Najeriya Ya Samu Miliyan 36 Saboda Amfani da Twitter Na Wata 1, Ya Saki Hoton Shaida
- Wani dan Najeriya ya bayyana makudan kudaden da ya samu daga Twitter a matsayin tukwicin amfani da dandalin na soshiyal midiya
- Mutumin ya samu zunzurutun kudi N36,000,000 daga Twitter a karshen wata kuma ya saki hoton bayanan bankinsa a matsayin shaida
- Ya mika godiyarsa ga Elon Musk, wanda ya yanke shawarar fara biyan masu amfani da Twitter bayan ya siye dandamalin a watannin baya
Wani dan Najeriya ya ba da mamaki a soshiyal midiya da irin makudan kudaden da ya samu daga Twitter (wacce aka fi sani da X a yanzu) a matsayin tukwicin godiya kan yawan amfani da dandamalin.
Twitter ya biya mutumin makudan kudade har N36,000,000 a karshen watan kuma ya wallafa hoton abun da ke cikin asusun bankinsa a matsayin shaida.
Ya godewa Elon Musk, dan kasuwa mai hangen nesa wanda ya yanke shawarar fara biyan masu amfani da Twitter kudi bayan ya siye dandalin yan watannin da suka gabata sannan ya sauya shi ya zama kafa mai dadin harka da amfani.
Dan Najeriya Ya Makale a Birtaniya Bayan Matarsa Da Ke Cin Amanarsa Ta Soke Bizarsa Don Auren Wani Daban
Biyan masu amfani da Twitter
Kamar yadda ya bayyana a jawabinsa da kuma ra'ayoyin manazarta, Elon Musk ya yanke shawarar fara biyan masu amfani da Twitter saboda wasu dalilai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Techcrunch, Musk yana so ya ba yan amana da masu yawan amfani da dandalin, wadanda ke kirkiran muhimman abubuwa da alaka da sauran mutane tukwici.
An dauki matakin ne domin jawo karin masu amfani dandalin da kuma masu daura talla a Twitter.
Mutane da dama sun kuma yi ikirarin cewa ya yi hakan ne don bai wa masu amfani da dandalin tallafi na musamman da bai wa Twitter karfi a kan sauran dandalin soshiyal midiya ta bangaren gasa.
Wasu kuma sun ce Musk yana son yin amfani da karfin Twitter a matsayin tushen labarai da kuma tasiri ta hanyar karfafawa masu yawan amfani da shi gwiwa.
Duba hoton a kasa:
Bayan Tafka Asara A 2022, Elon Musk Ya Dawo Matsayi Na 1 Da $250bn
A wani labari na daban, mun ji cewa mai kamfanin Twitter, Elon Musk ya dawo matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a duniya bayan asarar $200bn a shekara daya.
Musk ya rike matsayin nasa ne bayan adadin kudin da ya ke da shi ya kai har $250bn a jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta sake.
Asali: Legit.ng