Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum
- Masu garkuwa da mutane sun kai hari rukunin gidan El-rufai da ke yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja
- Yan bindigar sun yi awon gaba da wani mazaunin yankin mai suna Chinedu bayan sun yi ta harbi a iska
- Ciyaman na yankin Mai Baba Bego ya bayyana cewa yanzu suna zaman dar-dar ne don mutum biyar aka sace cikin yan watanni
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Mazauna yankin Kuchiko Resettlement Development Area (KRDA) da ke Bwari sun koka kan yawan sace-sacen mutane a cikin yankin.
Hakan ya biyo bayan lamarin da ya afku baya-bayan nan a safiyar Asabar, 2 ga watan Satumba, a yankin da aka fi sani da rukunin gidajen El-Rufai wato ' El-Rufai Estate'.
Yan bindiga sun sace mazaunin Abuja
Sace-sacen mutane don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a yankuna da dama a Najeriya cikin yan shekarun nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahin tsaro na daya daga cikin batutuwan da ke gaban shugaban kasa Bola Tinubu, wanda aka rantsar a watan Mayu.
Yan bindiga sun yi awon gaba da mutumin mai suna Chinedu daga gidansa da cikin rukunin gidajen.
Matar mutumin ta yi bayanin cewa masu garkuwa da mutanen da ke dauke da muggan makamai sun tisa keyar mijinta bayan sun haura ta katanga domin samun damar shiga cikin gidan nasu.
Jaridar Daily Trust ta nakalto matar na cewa:
"Sun yi ta harbi a iska domin tsorata iyalinmu da makwabta kafin suka yi awon gaba da mijina."
Mai Baba Bego, shugaban yankin wanda ya yi magana kan lamarin, ya ce mutane biyar aka sace cikin yan watannin da suka gabata, rahoton Naija News.
Baba Bego ya ce:
"Yanzu muna rayuwa cikin tsoro don babu wanda ya san wanene zai zama mutum na gaba."
Ba a samu jin ta bakin Josephine Adeh, jami'ar hulda da jama'a na rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Yan bindiga sun kashe masallata a masallacin Kaduna
A wani labarin, mun ji cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun farmaki masallata a wani masallaci a kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.
An bindige mutum biyar a cikin masallacin, yayin da aka tsinci gawarwakin sauran mutanen biyu a wasu wurare daban-daban a cikin yankin, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng