Basarake Ya Tilasta Matasa Sun Saki Matan Yan Bindigan Da Suka Kama a Zamfara

Basarake Ya Tilasta Matasa Sun Saki Matan Yan Bindigan Da Suka Kama a Zamfara

  • Kokarin da matasa suka yi a Zamfara na ganin sun ƙwato ƴan uwansu da ƴan bindiga a Zamfara ya tashi a tutar babu
  • Matasan dai sun kama matan ƴan bindigan da suka sace mutum shida a ƙauyen Birnin Magaji tare da shan alwashin ƙin sakinsu har sai an sako mutum shidan
  • Sai dai, wani basarake a ƙauyen ya tilasta su sakin matan Fulanin wanda hakan ya kawo tashin hankali a ƙauyen

Jihar Zamfara - An samu tashin hankali a ƙauyen Birnin Magaji na jihar Zamfara, bayan wani basarake ya tilasta matasan da suka cafke matan ƴan bindiga sun saki matan, cewar rahoton Vanguard.

Matasan dai sun cafke matan ƴan bindigan ne sannan suka sha alwashin cewa ba za su sake su ba, har sai sun sako musu mutum shida da suka sace a a ƙauyen.

Kara karanta wannan

Ruɗani: Matasa Sun Farmaki Wurin Ibada Gami Da Lalata Kayayyaki Da Dama, Bidiyonsu Ya Bayyana

Basarake ya tilasata matasa sun saki matan yan bindiga a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar ta nuna takaicinta kan sakin matan Fulanin guda biyu, inda ta nesanta kanta daga lamarin sannan ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan lamarin.

Ba ruwan gwamnatin Zamfara a lamarin

Duk da cewa manema labarai ba su samu jin ta bakin basaraken ba, Alhaji Ussaini Magaji, sakatarensa ya bayyana cewa za su yi magana kan lamarin a lokacin da ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani kwamishina a jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Birnin Magaji ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a saki matan ƴan bindigan ba kamar yadda ake yayatawa.

"Ba abu ba ne mai yiwuwa. Ta yaya gwamnan da ya ƙi tattaunawa da ƴan ta'adda zai bayar da umarnin sakin matan a daidai lokacin da mazajensu ke riƙe da mutum shida. Wannan ba gaskiya ba ne." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Ba Da Umarnin Rufe Makaranta Saboda Mummunan Laifin Da Aka Aikata a Cikinta

Ya ƙara da cewa gwamnatin ba ta da masaniya cewa an kama matasan da suka riƙe matan Fulanin, inda ya ƙara da cewa za a gudanar da bincike.

Rahotannin sun bayyana cewa bayan basaraken ya bayar da umarnin sakin matan, an ɗauke su akan babura zuwa wani daji domin komawa wajen mazajensu.

Sakin matan dai ya janyo tashin hankali da sanya shakku musamman a zukatan ƴan uwan mutum shidan da aka sace waɗanda har yanzu suna hannun ƴan bindiga.

PDP Ta Bankado Tuggun APC a Zamfara

A wani labarin kuma, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara ta zargi jam'iyyar APC da shirin sanya ƴan majalisar dokokin jihar su tsige gwamna Dauda Lawal.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa APC na shirin yin amfani da kuɗi domin sanya ƴan majalisar su tsige gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng