Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu

Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta tsuma zukata yayin da ta dawo Najeriya sannan ta yi wa saurayinta wanda yake aikin kanikanci a bakin haya bazata
  • A cewarta, matashin ya dauki nauyin karatunta zuwa kasar Birtaniya domin ta yi digiri na biyu, amma sun dauki tsawon shekaru basa jin doriyar juna
  • Wani bidiyo mai motsa zuciya ya nuno haduwar masoyan kuma ya burge masu amfani da soshiyal midiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bakaniken bakin hanya mai suna Segun, ya cika da farin ciki yayin da budurwarsa, wacce ya dauki nauyin karatunta zuwa kasar Birtaniya ta dawo bayan shekaru uku.

Wani mai watsa shirye-shirye a TikTok Theo Ayoms, wanda ya taimaka wajen sake hada su, ya wallafa bidiyon mai tsuma zuciya a soshiyal midiya.

Matashiya ta hadu da saurayinta bakanike bayan shekaru a Turai
Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @theoayoms
Asali: TikTok

Segun baya tsammanin ganin Ngozi

Da Theo ya yi hira da shi, bakaniken ya tabbatar da cewa shine ya dauki nauyin karatun Ngozi domin ta yi digiri na biyu a Birtaniya, wanda ya kamata ace ta kammala a cikin shekara daya da watanni.

Kara karanta wannan

Kishi: Wani Matashin Saurayi Ya Buga Wa Budurwarsa Guduma Har Lahira Kan Abu 1

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ya cika da mamaki cewa basu kara jin doriyar juna ba, sannan shekara daya ya zama shekaru uku amma bai cire tsammani ba.

Ngozi ta dawo a ranar zagayowar haihuwar Segun

A ranar zagayowar haihuwarta, Ngozi ta dawo da kek da kuma muradin gyara soyayyarsu, da kuma sauya rayuwarsa.

Ngozi ta kuma bayyana cewa saurayin nata ya tallafawa karatunta yayin da take Najeriya, tana mai cewa yanzu tana cikin daula a turai, kasancewar ta samu aiki mai kyau.

Bidiyon haduwarsu ya tsuma zukata.

Kalli bidiyon a kasa:

Labarin Segun da Ngozi ya tsuma zukata

ggibpablogh ya ce:

"Kallon wannan bidiyon har zuwa karshe ya sa ni kuka kuma na taya su farin ciki."

mercury lord ta ce:

"Samun saurayi a Birtaniya na da wahala kuma ta fara tsufa shine dalilin da yasa ta dawo gare shi."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauyoyi Da Yan Uwansa

Solomon ya ce:

"Sun karya mata zuciya a UK ta dawo ga wanda bata alfahari da shi a baya."

davidoladejo218 ya ce:

"Nagode Allah ma wannan yarinyar kuma na yarda cewa ba za ta taba danasanin wannan ba da sunan Yesu."

Mijina baya kwantawa da ni tsawon shekaru biyu

A wani labarin kuma, wata matar aure mai shekaru 25, Ruqayya Mukhtar ta fada ma wata kotun Shari'a da ke Rigasa, jihar Kaduna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, cewa mijinta bai kwanta da ita ba tsawon shekaru biyu.

Mai karar wacce ta nemi kotu ta raba aurenta da wani mai Naziru Hamza ta kuma koka cewa mijin nata na cin zarafi da mutuncinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng