Ministan Wasanni Ya Koma Cikin Filin Wasa Na MKO Abiola Da Ke Abuja Da Zama

Ministan Wasanni Ya Koma Cikin Filin Wasa Na MKO Abiola Da Ke Abuja Da Zama

  • John Enoh wanda shi ne sabon ministan wasanni ya mayar da ofishinsa cikin filin wasa na MKO Abiola da ke AbujaJohn Enoh wanda shi ne sabon ministan wasanni ya mayar da ofishinsa cikin filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja
  • Enoh ya ce ya yanke wannan shawarar ce tun bayan zagayawa cikin filin wasan a ranar da ya shiga ofis inda ya ce hakan ya zama dole
  • Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya yi wa ministocin gargadin cewa duk wanda bai tabuka komai ba zai rasa mukaminsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Sabon ministan wasanni a Najeriya, John Enoh ya bayyana dalilin da yasa ya mai da ofishinsa filin wasa na MKO Abiola a Abuja.

Yayin da ya ke magana a ranar Alhamis 31 ga watan Agusta, ministan ya ce ya yi haka ne don sanya idanu kan harkokin wasanni.

Kara karanta wannan

“Za a Iya Korarka Daga PDP” ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Kaca-Kaca da Wike

Ministan wasanni ya koma filin wasa da zama a Abuja
Ministan Wasanni Ya Fadi Dalilin Komawarsa Cikin Filin Wasa Na MKO Abiola. Hoto: Naira Sports.
Asali: Facebook

Meye dalilin komawarsa filin wasa?

Ya ce ya yanke hukuncin hakan ne bayan ya zagaya cikin filin wasan a ranar da ya shiga ofis, cewar TheCable.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Na zagaya cikin filin wasan MKO Abiola, na yanke hukunci madadin ci gaba da zama a sakatariya, zai fi kyau na dawo cikin filin wasan.
“Na riga na dauki matakin tun tuni, bukata na shi ne ma’aikatar wasanni ta yi aiki yadda ya kamata kuma mu za mu saka ta yi kyau.
“A cikin filin wasan ne mu ke da kaso 90 na dukkan bangarorin wasanni da suka hada da ‘yan kwallo da masu motsa jiki da sauransu.”

Ya ce komawarsa filin wasan ya zama dole

Ministan ya ce dole ya maida ofishinsa cikin filin wasan don tabbatar da komai na tafiya dai-dai yadda ya dace.

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

Ya ce ya tura takarda ga sakataren din-din-din na ma’aikatar wasanni kan cewa dole dukkan bangarorin wasanni su dawo cikin filin wasan.

Enoh ya ce ya na son ya bunkasa harkar wasanni yadda za ta je inda babu damarmaki na nuna bajintar matasa musamman a wuraren talakawa, Vanguard ta tattaro.

Tsohon Ministan Wasanni Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, tsohon ministan wasanni, Bala Bawa Ka'oje ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 60 a duniya.

Kakakin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Ademola Olajire shi ya bayyana mutuwar Ka'oje a cikin wata sanarwa.

Babban Sakataren hukumar NFF, Mohammed Sanusi da sauran manyan ma'aikata na hukumar sun samu halartar jana'izar mutuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.