Tsegumi: Ali Nuhu zai zama ministan wasanni da matasa a gwamnatin Buhari

Tsegumi: Ali Nuhu zai zama ministan wasanni da matasa a gwamnatin Buhari

- Wasu rahotanni da muka samu sun nuna cewa, akwai yiwuwar jarumi Ali Nuhu zai iya zama daya daga cikin Ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa ta cewa gwamnonin arewa sun nuna goyon bayansu akan tsayar da jarumin a matsayin Ministan matasa da wasanni

- Jarumin dai yayi kokari kwarai da gaske wajen taya shugaban kasar kamfen a yankin arewacin Najeriya a lokacin yakin neman zabe

Wani labari da yake ta yawo a shafukan sada zumunta na zamani, irinsu Facebook, Twitter da Instagram, sun nuna cewa akwai yiwuwar fitaccen jarumin wasan Hausa na Kannywood din nan, Ali Nuhu, zai iya zama Ministan Wasanni da Matasa a cikin jerin Ministocin shugaba Buhari.

Wannan labari ya fito ne bayan wata jita-jita da aka yada ta cewar wasu daga cikin manyan gwamnonin arewa sun nuna goyon bayansu dari bisa dari ga fitaccen dan wasan domin ya zama daya daga cikin Ministocin shugaba Buhari a kasar nana.

KU KARANTA: Tirkashi: Na sha turawa mijina kanwata ya kwanta da ita ba tare da saninshi ba - Hassana ta bayyana sirrinta

Fitaccen jarumin dai ya nuna soyayyarsa matuka ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatin APC, domin kuwa yana daya daga cikin jiga-jigan wadanda suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da babbar jam'iyyar APC kamfen a yankin arewacin kasar nan.

Wasu daga cikin wadandan suka taya shugaban kasar kamfen a cikin 'yan wasan Hausan sun hada da shahararren mawakin nan Rarara, Adamu Zango, Aminu Ala, Nazifi Asnanic da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng