Tinubu Ya Ware Naira Biliyan 50 Don Sake Gina Arewacin Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya sake ware wasu makudan kudade don sake gina yankin Arewacin Najeriya da ta sha fama da matsalar tsaro
- Tinubu ya ware makudan kudade har Naira biliyan 50 musamman ga Arewa maso Yamma da kuma Gabas don taimakawa jihohin
- Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasar shi ya bayyana haka a yau Alhamis a fadar shugaban da ke Abuja yayin wata ganawa
FCT, Abuja – Sugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ware Naira biliyan 50 don sake gina Arewacin kasar da ratsin tsaro ya dai-daita.
Shugaban ya ware kudaden ne musamman don Arewa maso Yamma da kuma Gabas wadanda su kafi fuskantar matsalar tsaro.
Meye Tinubu ya yi wa Arewa?
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya bayyana haka a fadar shugaban kasa a yau Alhamis 31 ga watan Agusta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shettima ya ce gwamnatinsu ta himmatu wurin mai da hankali ta hanyar da za a kawo karshen matsalar tsaro, PM News ta tattaro.
Yayin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya yi magana kan irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki tun bayan cire tallafin mai.
Ya ba da tabbacin cewa a irin tsare-tsaren da ya ke kawo wa zai taimaka wurin daidaita tattalin arzikin kasar wanda jama’ar Najeriya za su fi mora.
Wane tabbaci Tinubu ya bai wa Arewa da Najeriya?
Ya ce:
“Najeriya na kan turba mai kyau, rarrabe-rarraben da mu ke da su zai kai mu ga nasara ne ba matsala ba, za mu gina kasar da ‘ya’yan mu za su yi alfahari da ita.”
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubkar yayin jawabinsa, ya nuna goyon bayansa dari bisa dari ga shugaban kasa inda ya ce mutum na iya zuwa mataki ne kawai idan ubangiji ya yarda ba dan Adam ba.
Sultan ya ce a ko wane lokaci a shirye su ke don wata bukata ko shawara ko kuma wata taimako daga shugaban, cewar BBC Hausa.
Ya ba da shawara kan raba tallafi inda ya bukaci a sanya ido sosai don ganin ya isa inda ya kamata yaje.
Najeriya Ta Biya Bashin Dala Biliyan 1.17 A Watanni 6
A wani labarin, Najeriya ta biya bashin fiya da Dala biliyan 1.17 ga kasashen Sin da kuma Faransa.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya sha alwashin kawo karshen dogaro da bashi da kasar ke yi.
Asali: Legit.ng