Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja

Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja

- Wata motar tanka cike da man fetur ta kama da wuta bayan ta kara da wata motar tirela

- Lamarin wanda ya afku a yankin Lambata, jihar Neja ya yi sanadiyar konewar gidaje, motoci da wasu dukiyoyi

Wata motar tanka cike da man fetur ta kama da wuta bayan ta kara da wata motar tirela, inda hakan ya yi sanadiyar konewar gidaje, motoci da wasu dukiyoyi.

Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Satumba da misalin karfe 11:00 na dare, jaridar The Nation ta ruwaito.

Zuwa safiyar yau Litinin, 7 ga watan Satumba babu cikakken bayani kan yawan asarar da aka yi.

Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja
Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja Hoto: The Nation
Asali: UGC

An tattaro cewa tirelar ta kara da tankar inda hakan ya sa tirelar faduwa sannan ta kama da wuta a nan take.

KU KARANTA KUMA: Kada ku koma ajujuwa idan aka bude makarantu, NUT ga malamai

Gidaje da dama, shaguna da motoci sun kone kurmus kafin a kira masu kashe gobara daga Suleja domin su daidaita lamarin.

Hukumar kiyayye haddura ta kasa (FRSC) ta daura alhakin hatsarin kan kwacewar birkin motocin.

Zuwa yanzu dai ba a san yawan mutanen da suka rasa ransu ba.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa rayuka sun salwanta yayinda da dama sun jikkata a wani mumunan hadarin da ya auku a gadar saman Otedola dake jihar Legas da safiyar Alhamis, 21 ga Mayu, 2020.

Mun tattaro cewa hadarin ya faru ne misalin karfe 8 na safe.

Hukumar kiyaye hadura na jihar Legas, LASTMA, ta bayyana cewa hadarin ya auku ne tsakanin motar Tanka da wata motar Bas mai dauke da fasinjoji 10.

A jawabin da hukumar ta saki, tace: "Mumunan hadari ya auku ne kan gadar Otedola, yayinda ake kokarin shiga Berger tsakanin wata Tanka da motar Bas kirar Mazda."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng