Dalilin da Yasa Aka Ga Faston Coci Na Rike da AK-47 a Abuja, Coci Ya Yi Karin Haske

Dalilin da Yasa Aka Ga Faston Coci Na Rike da AK-47 a Abuja, Coci Ya Yi Karin Haske

  • Biyo bayan kama fasto Uche Aigbe, cocin House on the Rock ya yi bayan dalilin da yasa aka ga faston dauke da mugun makami AK-47 a bainar jama’a
  • Cocin ya ce, faston ya rike fankon bindigan ne da babu komai a cikinsa don nunawa mabiyansa tasirin tsare imani
  • Duk da haka, cocin ya ga laifin faston, ya kuma bayyana neman afuwa a madadinsa tare da bayyana dana-sanin wannan aikin

FCT, AbujaHouse on the Rock, wani fitaccen cocin addinin Kirista a Najeriya ya bayyana cewa, fastonsa, Uche Aigbe na Abuja ya dauki bindiga AK-47 a filin ibada ne don nunawa mabiyansa aya.

Cocin ya yi wannan karin hasken ne a ranar Litinin 13 Faburairu, 2023 da yamma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: 'Yan sanda sun dauki mataki kan faston da aka ga ya rataye AK-47 a Abuja

Legit.ng Hausa ta ruwaito a baya cewa, faston ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta tun bayan da aka ganshi ranar Lahadi yana rataye da wani mugun makami.

Dalilin da yasa fasto ya rike makami
Dalilin da Yasa Aka Ga Faston Coci Na Rike da AK-47 a Abuja, Coci Ya Yi Karin Haske | Hoto: @ogundamisi
Asali: Twitter

Da yake jawabi, an ji faston na bayanai masu kama da sukar wasu malaman addinin Kirista da basa jituwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai yake cewa:

“Wannan yasa na ke ganin ya kamata mu rike bindigogi don kare kanmu. Zan zo musamman don wasu da ke bacci a wannan cocin.”

Fasto ya nemi afuwa

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, cocin ya ce faston ya zo da bindiga wurin wa’azinsa ne domin nunawa mabiya tasirin yakar munanan dabi’u da makami.

Cocin ya kuma yi karin haske da cewa, faston ya yi hakan ne don nunawa duniya yadda ake tsare imani, kuma bindigar babu komai a cikinta.

Kara karanta wannan

Zargin Darektan Yakin Zaben Bola Tinubu a 2023, Ya Jefa Shi a Hannun Dakarun DSS

Daga nan ne cocin ya ce zai tsawatarwa faston, kana yana ba kasa da hukumomin tsaro hakurin wannan lamari, rahoton Within Nigeria.

Har yanzu dai ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta basu huce da daukar zafin da suka yi ba kan wannan batu na fasto mai bindiga.

‘Yan sanda sun kama faston

A bangare guda, kunji yadda hukumar ‘yan sandan Najeriya suka yi ram da faston don bincikarsa.

Hakazalika, an gano jami’in da ya dauki bindigar da aka bashi don aikin kasa ya ba faston don wata manufa.

An ba da shawarin garkame faston tare da dakatar da jami’in dan sandan da ke da hannu a wannan mummunan aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel