Dan Takarar Shugaban Kasa a SDP Ya Bayyana Babban Kuskure 1 Na Buhari da Tinubu Ke Tafkawa a Yanzu

Dan Takarar Shugaban Kasa a SDP Ya Bayyana Babban Kuskure 1 Na Buhari da Tinubu Ke Tafkawa a Yanzu

  • Wani babban lauya a Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP ya nuna matukar damuwa dangane da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki
  • Prince Adewole Adebayo ya ji tsoron cewa Tinubu na bin hanyar da magabacinsa ya bi dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki
  • Yayin da yake martani ga mulkin Tinubu na tsawon watanni uku, Adewole ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mummunar manufa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Prince Adewole Adebayo, dan takarar jam’iyyar SDP a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana bin tafarkin Muhammadu Buhari, wanda ya gabace shi, ta fuskar ji da tattalin arziki.

Dan siyasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake waiwaye ga tsawon watanni uku da shugaban kasar ya yi yana mulki da kuma yadda tattalin arzikin kasar ya dagule a karkashin Tinubu.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

Da yake magana kan halin da kasa ke ciki da kuma kokarin Tinubu zuwa yanzu, Adewole ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mummunar manufa, inji rahoton Daily Trust.

Kuskuren Buhari Tinubu ke tafkawa
Buhari da Bola Tinubu a wurin wani taron APC | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Yadda ake ba da tallafi a wasu kasashe

Ya ce a inda tattalin arzikin kasa ke gaba, duk abin da ke sa tattalin arzikin ya bunkasa ana ba da tallafi a kansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“A Amurka, suna ba da tallafi kan magunguna, suna ba da tallafi a kiwon lafiya; a Burtaniya, suna ba da tallafi a sufuri."

Adebayo ya kuma bayyana rashin daidaito game da yadda shugaban kasa ya cire tallafin, ya kuma bukaci Tinubu ya gyara kuskuren, yana mai cewa bai dace a kuntatawa ‘yan Najeriya ba.

Ya kuma yi barazanar cewa jam’iyyar SDP za ta karbi ragamar mulki a shekarar 2027 matukar ba a yi wani abu na inganta shugabanci a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana

Maza sun gaza, mata injiniyoyi sun ce a ba su damar gyara matatun mai

A wani labarin, kungiyar kwararrun mata injiniyoyi ta Najeriya (APWEN) ta shaida wa shugaban kasa Bola Tinubu cewa injiniyoyi mata za su iya gyara matatun man kasar nan da suka lalace cikin shekara guda.

Shugabar kungiyar ta APWEN, Atinuke Owolabi, ta bayyana haka ne a yayin taron lacca da taron shekara-shekara na kungiyar a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta a Legas.

Ta ce injiniyoyi mata a Najeriya suna da karfin farkar da matatun mai da ke barci a cikin shekara guda, inji rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.